Mummunar gobara ta kona gidan wani dan majalisar wakilai daga jahar Zamfara

Mummunar gobara ta kona gidan wani dan majalisar wakilai daga jahar Zamfara

Hukumar kashe gobara ta jahar Zamfara ta sanar tare da tabbatar da tashin gobara a gidan wani dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe, Alhaji Kabiru Mai Palace, dake garin Gusau a ranar Talata.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito mataimakin darakta a hukumar, Abdullahi Jibo ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da wakilinta, inda yace wutar ta tashi ne a gidan dake unguwar Yarima, cikin garin Gusau.

KU KARANTA: Mutane 6 sun mutu a sanadiyyar harin yan bindiga a jahar Kaduna

Mummunar gobara ta kona gidan wani dan majalisar wakilai daga jahar Zamfara
Mai Palace
Asali: Facebook

Malam Jibo yace alamu sun nuna wutar lantarki ne ya yi sanadiyyar tashin gobarar, saboda a cewarsa da misalin karfe 10:30 na safiyar talata suka samu kiranye daga unguwar game da tashin gobarar, inda yace ba tare da bata lokaci ba jami’ansu suka isa gidan, suka kuma kashe wutar.

“Cikin ikon Allah ba’a samu asarar rai ko rauni ba, kuma mun samu daman dauke motoci guda biyu daga gidan.” Inji shi. Haka zalika Malam Jibo ya yi kira ga jama’an jahar Zamfara da su dinga kula yayin amfani da kayan wutar lantarki, kuma su sanar dasu cikin lokaci idan an samu tashin gobara.

Shi ma wani ma’aikacin gidan dan majalisar mai suna Mustafa Hassan ya bayyana gobarar da abin tsoro, inda yace: “Da misalin karfe 10 na safiya wutar ta tashi, kuma ta cinye gidan gaba daya, dukiya ta miliyoyin nairori sun salwanta a dalilin haka. Abin takaici.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban burin kungiyar ta’addanci na Boko Haram shi ne kawo rarrabuwar kai a tsakanin yan Najeriya, tare da gwara kawunan yan kasa, don haka ya yi kira ga yan Najeriya su bari wannan buri ya yi tasiri.

Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da hadiminsa a kan harkokin watsa labaru, Femi Adesina ya fitar a ranar Talata, 4 ga watan Feburairu inda ya yi alhinin mutuwar shugaban kiristoci na karamar hukumar Michika, Rabaran Lawan Andimi a hannun Boko Haram.

Buhari ya bayyana damuwarsa yadda duk da nisan mil 60 dake tsakanin garin Chibok da cocin Andimi, amma sai da mayakan yan ta’adda suka kama shi tare da yin garkuwa da shi, daga bisani kuma suka kashe shi.

“Tun bayan darewata mukamin shugaban kasa a shekarar 2015, mun amso yan matan Chibok 107, har yanzu muna cigaba da kokarin amso sauran, amma matsalar ita ce an samu rabuwar kai a Boko Haram, wanda hakan ya haifar da bangarori da dama, wanda suke kai hare hare bisa radin kansu." Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel