Yanzu-yanzu: Dan sanda ya kashe kansa a Legas

Yanzu-yanzu: Dan sanda ya kashe kansa a Legas

Wani dan sanda mai suna Eze ya rataye kansa a cikin dakin tsare wadanda ake zargi a caji ofis na sashin masu binciken manyan laifuka na 'yan sada (CIID) da ke Yaba a Legas.

The Punch ta ruwaito cewa dan sandan da ke aikin gadi a daya daga cikin kamfanonin dan Dangote an kama shi ne bayan ya harbe wani mutumi har lahira.

Yanzu-yanzu: Dan sanda ya kashe kansa a caji ofis a Legas
Yanzu-yanzu: Dan sanda ya kashe kansa a caji ofis a Legas
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Turai Yar'adua ta ziyarci Aisha Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Wata amintaciyar majiya ta ce: "An kawo shi ofishin binciken manyan laifuka ne domin a zurfafa bincike kana a gurfanar da shi.

"Amma ya rataye kansa a cikin dakin ajiye wadanda ake zargi misalin karfe 2 na dare. Yana aiki ne da daya daga cikin kamfanonin Dangote kuma ya harbe wani mutumi har lahira."

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun 'yan sandan Legas, Bala Elkana ya ce zai tabbatar da gaskiyar lamarin sannan ya kira waya.

Bai kira ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel