Ba mu da niyyar korar ma'aikata a yanzu - Gwamnatin Tarayya

Ba mu da niyyar korar ma'aikata a yanzu - Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba ta da niyyar kora ko sallamar ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Akanta Janar na tarayya, Alhaji Ahmed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja yayin jawabin da ya yi a taron Lunch Time Reform Seminar 2020 da aka yi na farko wannan shekarar.

Hukumar gudanar da sauye-sauye a ayyukan gwamnati (BPSR) ne ta dauki nauyin shirya taron na wannan shekarar da ya mayar da hankali kan bullo da sabbin dabarun zamani na kulawa da kudade a kasar.

Ba mu da niyyar korar ma'aikata a yanzu - Gwamnatin Tarayya
Ba mu da niyyar korar ma'aikata a yanzu - Gwamnatin Tarayya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Turai Yar'adua ta ziyarci Aisha Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Idris ya ce bai amince da wadanda ke ganin cewa ma'aikatan gwamnati sun yi yawa ba, abinda ya ke gani shine a inganta ayyukan domin kallubale ne mai fuskoki da dama domin a lokuta da yawa ba wai rashin iya aikin bane ko wanda za suyi aikin sai dai turo mutanen da ya dace zuwa wuraren da ya dace da su.

Idris ya ce "Kamar yadda ya fadi muna da karancin kwararru kaman likitoci, masu jinya da sauran masu aikin lafiya. Ba mu cimma sauran kasashe da suka cigaba ba. Ba mu da isasun 'yan sanda.

"Muna da matsalar rashin tsaro saboda haka muna bukatan karin 'yan sanda. Ya kamata gwamnati ta bullo da tsari. Saboda haka ma'aikatan gwamnati ba su yi yawa ba matalar shine inganta aikin kuma ya kamata a magance lamarin.

"Mu cigaba da neman yadda za mu warware matsalar. Akwai bangarori da yawa da ba su da isasun ma'aikata kuma can ya kamata a tura musu ma'aikata."

Ya kuma ce akwai bukatar a cigaba da tsare-tsaren yi wa fannin kudi garambawul ta hanyar bayar da hadin kai da tabbatarwa gwamnatocin gaba ba za su yi watsi da shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel