Mutane 6 sun mutu a sanadiyyar harin yan bindiga a jahar Kaduna

Mutane 6 sun mutu a sanadiyyar harin yan bindiga a jahar Kaduna

Gungun miyagu yan bindiga sun bindige mutane 6 a wasu hare hare da suka kai a kauyen Kakangi dake cikin karamar hukumar Birnin Gwari, kamar yadda wani mazaunin yankin ya tabbatar.

Jaridar Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata, inda wani jami’in fadar Sarkin Birnin Gwari Abdullahi Bature ya bayyana cewa sun tare yan bindigan ne yayin da suka dauko wasu garken shanu da suka sato daga jahar Neja.

KU KARANTA: Gwamnan Ondo ya ziyarci Villa, ya nemi Buhari ya samar da dokar halasta tabar wiwi

“Yan bindigan sun kashe yan banga 6 a yayin musayar wuta da ya kaure a tsakaninsu domin su kwace dabbobin da suka sato, yan bangan sun sake gangami don fuskantar yan bindigan, amma sun fi karfinsu.” Inji shi.

Haka zalika a hannu guda, wasu gungun yan bindiga da yawansu ya kai 100 sun kai farmaki a kan babura zuwa wasu kauyukan jahar Zamfara, inda suka yi ta harbe harbe tare da farfasa gidajen jama’a suna sata da kuma banka musu wuta.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana daga cikin kauyukan da yan bindigan suka kai ma hari akwai Yar Talata inda suka kashe mutane hudu da kauyen Dan Fili inda suka kashe mutum 1, sa’annan suka garzaya zuwa wasu kauyuka 5.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban burin kungiyar ta’addanci na Boko Haram shi ne kawo rarrabuwar kai a tsakanin yan Najeriya, tare da gwara kawunan yan kasa, don haka ya yi kira ga yan Najeriya su bari wannan buri ya yi tasiri.

Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da hadiminsa a kan harkokin watsa labaru, Femi Adesina ya fitar a ranar Talata, 4 ga watan Feburairu inda ya yi alhinin mutuwar shugaban kiristoci na karamar hukumar Michika, Rabaran Lawan Andimi a hannun Boko Haram.

Buhari ya bayyana damuwarsa yadda duk da nisan mil 60 dake tsakanin garin Chibok da cocin Andimi, amma sai da mayakan yan ta’adda suka kama shi tare da yin garkuwa da shi, daga bisani kuma suka kashe shi.

“Tun bayan darewata mukamin shugaban kasa a shekarar 2015, mun amso yan matan Chibok 107, har yanzu muna cigaba da kokarin amso sauran, amma matsalar ita ce an samu rabuwar kai a Boko Haram, wanda hakan ya haifar da bangarori da dama, wanda suke kai hare hare bisa radin kansu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel