Idan aka sake sace kudaden Abacha, sai kun biya – Amurka ga Najeriya

Idan aka sake sace kudaden Abacha, sai kun biya – Amurka ga Najeriya

Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi gwamnatin Najeriya game da kudaden da tsohon shugaban kasar Najeriya marigayi Janar Sani Abacha ya jibge a bankunan kasashen waje, inda tace Najeriya za ta biya kudaden idan har ta bari aka sake sace kudin.

A ranar Litinin, 3 ga watan Feburairu ne gwamnatin Amurka, Najeriya da Bailiwick na Jersey suka rattafa hannu kan yarjejeniyar maido da dala miliyan 308 da Abacha ya jibge a wasu bankunan kasashen waje.

KU KARANTA: Gwamnan Ondo ya ziyarci Villa, ya nemi Buhari ya samar da dokar halasta tabar wiwi

An sace wadannan kudade ne ta bankunan kasar Amurka, inda aka jibgesu a asusun bankin kasar Jersey da sunan wani kamfani Doraville Properties Corporation, wanda yaron Abacha ke shugabanta.

A shekarar 2014 ne wata kotun Amurka ta bayyana kudin a matsayin haramtattu da aka sace a tsakanin shekarun 1993 da 1998, daga nan babban lauyan Jersey ya nemi daman daskarar da asusun bankin Doraville, kuma kotu ta sahhale masa.

Ana zargin Abacha da abokansa na kusa dun wawure makudan kudade daga lalitar gwamnati a miliyoyin daloli a zamanin mulkinsa wanda hakan ya kawo nakasu ga tattalin arzikin kasar, daga cikin wadanda suka kwashe kudaden akwai yaransa Ibrahim da Muhammad, da wasu yan uwansa na kusa.

Wasu daga cikin kasashen da aka kwato kudaden Abacha sun hada da Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus, Switzerland, Lichtenstein da kuma Luxembourg, a shekarar 2018 aka fara sabon tsare tsaren maido da kudaden Najeriya, sai a cikin makonnan aka kawo karshen tsare tsaren da rattafa hannu.

Mai magana da yawun Amurka, Morgan Ortagus ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka kulla ta tanadi a kashe kudaden wajen yi ma yan Najeriya aiki, kuma gwamnatin Najeriya za ta kafa kwamitin sa ido don tabbatar gaskiyar yadda aka kashe kudaden.

Haka zalika Ortagus yace “Mayar da wadannan kudade ga Najeriya ya tabbatar da bukatar hadin kai tsakanin kasashen duniya domin yaki da rashawa, tare da mayar da kudaden sata cikin tsari na gaskiya da gaskiya.

“Bugu da kari ya yi daidai da alkawarin da Amurka da Najeriya suka daukan ma juna a shekarar 2017 yayin taron mayar da kudaden sata na duniya wanda kasashen Amurka da Birtaniya suka dauki nauyi.

“Wannan yarjejeniya ya tabbatar da muhimmancin da gwamnatin Amurka ta baiwa yaki da rashawa, kuma muna maraba da manufar shugaban kasa Buhari wajen yaki da rashawa, kuma zamu cigaba da baiwa kungiyoyi masu zaman kansu goyon baya domin su yaki rashawa a Najeriya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng