Shugaban karamar hukuma ta raba wa mata kayan gini (Hotuna)

Shugaban karamar hukuma ta raba wa mata kayan gini (Hotuna)

Shugaban karamar hukumar Nsukka, Honarabul Chinwe Ugwu da a baya ya ke raba wa mata baro ta fara rabon kayayakin gini da suka hada da cebur da kwanon daukan kankare a karamar hukumar ta.

Wani mai amfani da shafin Facebook, Chijinkem Ugwuanyi da ya wallafa hotunan rabon kayan tallafin ya yi ikirarin cewa shugaban karamar hukumar ta rabar da kwanon daukan kankare 50, cebur 50 da kuma cokalin plasta 20.

Shugaban karamar hukuma ta raba wa mata kayan gini (Hotuna)
Shugaban karamar hukumar Nsukka tare da mata da ta bawa tallafin kayan gini
Asali: Facebook

Shugaban karamar hukuma ta raba wa mata kayan gini (Hotuna)
Shugaban karamar hukumar Nsukka yayin da ta ke gabatar da tallafin kayan gini ga mata a karamar hukumar ta
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Turai Yar'adua ta ziyarci Aisha Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Ya rubuta cewa;

No #Movement

Wayyo Allah! Wannan irin abin kunya haka?

Zalunci ba na wasa ba...

Azzaluman 'yan siyasan Najeriya...

Kuma dai, Hon. Chinwe Ugwu shugaban karamar hukuma Nsukka ya sake rabon kwanukan daukan kankare 50, cebur 50 da cokalin plasta 20 a matsayin tallafi.

Mene ke damun wadannan mutanen? Kwanakin baya matan nan ta raba Wheelbarrow a matsayin tallafi

'Yan siyasa marasa basira daga yankin Enugu ta Arewa, suna raba wa mutane cebur da kwangiri suna karfafa musu gwiwa su cigaba da shan wahala.

Shugaban karamar hukuma ta raba wa mata kayan gini (Hotuna)
Hotunan kayan gini da aka raba wa mata a karamar hukumar Nsukka
Asali: Facebook

Muna rayuwa cikin zalunci, inda 'yan siyasa za su jefa maka yunwa daga bisani su ba ka abinci, za su cije ka sannan su baka hakuri...

Ya ke shugaban karamar hukuma, mene yasa ki ke bawa mutane kwarin gwiwa su cigaba da wahala? ... Shin ko za ki fara bawa 'ya'yan kayan ginin su fita su yi aikin karfi

Na kasa fahimtar wannan abin, Muna bawa mata kwarin gwiwa su fita aikin karfi ne?

Wannan ba tallafi bane, wannan bauta ne.

Shugaban karamar hukuma ta raba wa mata kayan gini (Hotuna)
Shugaban karamar hukuma ta raba wa mata kayan gini (Hotuna)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel