Burin Boko Haram shi ne ta kawo rabuwar kai a tsakaninmu – Buhari ga yan Najeriya

Burin Boko Haram shi ne ta kawo rabuwar kai a tsakaninmu – Buhari ga yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban burin kungiyar ta’addanci na Boko Haram shi ne kawo rarrabuwar kai a tsakanin yan Najeriya, tare da gwara kawunan yan kasa, don haka ya yi kira ga yan Najeriya su bari wannan buri ya yi tasiri.

Punch ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da hadiminsa a kan harkokin watsa labaru, Femi Adesina ya fitar a ranar Talata, 4 ga watan Feburairu inda ya yi alhinin mutuwar shugaban kiristoci na karamar hukumar Michika, Rabaran Lawan Andimi a hannun Boko Haram.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta shiga yarjejeniya da kasar Amurka game da dawo da kudaden Abacha gida

Buhari ya bayyana damuwarsa yadda duk da nisan mil 60 dake tsakanin garin Chibok da cocin Andimi, amma sai da mayakan yan ta’adda suka kama shi tare da yin garkuwa da shi, daga bisani kuma suka kashe shi.

“Tun bayan darewata mukamin shugaban kasa a shekarar 2015, mun amso yan matan Chibok 107, har yanzu muna cigaba da kokarin amso sauran, amma matsalar ita ce an samu rabuwar kai a Boko Haram, wanda hakan ya haifar da bangarori da dama, wanda suke kai hare hare bisa radin kansu.

“Ina godiya ga jami’an tsaronmu da kuma gudunmuwar da muke samu daga rundunar Sojin Birtaniya da rundunar Sojan Amurka saboda irin nasarar da suke samu a filin daga. Abu ne mai saukin fahimtar manufar yan ta’adda, shi ne su dinga kai hare hare wurare masu rauni domin raba kawunan Musulmai da Kiristoci.

“Don haka nake kira da kada mu yarda da wannan, kada mu yarda su raba mu da abin daya hada mu, daga bautan Ubangiji, addini, dangin juna, abota da kuma yafiya ga juna. Suna yin haka ne saboda sun gaza wajen kama wani sashi a kasar nan, don haka suka gwammace su gwara kawunanmu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Hukumar yaki da rashawa da dangoginsu, ICPC, ta fitar da wani sanarwar dake dauke da sabbin bayanai game da aikin da ta sanar da za ta dauka a cikin sabuwar shekarar 2020, wanda a kwanakin baya ta sanar ma yan Najeriya masu sha’awa su nema.

Hukumar ta bayyana cewa biyo bayan kulle amsan takardun masu sha’awar aikin, ta kidaya mutane 376,631 daidai da suka nuna sha’awarsu na yin aiki a cikinta, sai dai hukumar ta kara da cewa gurabe 220 take dasu kacal.

ICPC ta bayyana haka ne a shafin ta na Facebook, inda tace akwai ire iren mutanen da take bukatar dauka daga cikin wadanda suka nemi ayyukan, daga cikinsu akwai wadanda suka karanci kididdigar kudi, sharia, tsimi da tanadi, kimiyyar kwamfuta, lissafi, jarida, zane, da sauran manyan kwasa kwasai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel