Kashi 90% na mutanen da Boko Haram ke kashewa Musulmai ne - Buhari

Kashi 90% na mutanen da Boko Haram ke kashewa Musulmai ne - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kashi 90 na wadanda Boko Haram ke kashewa Musulmai ne sabanin rade-radin da wasu kungiyoyi ke cewa Kirista ake kashewa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan a jawabin da saki a mujjalar Kirista 'Christianity Today'.

Buhari yace: "Har yanzu bamu samu nasarar yakan karya da gaskiya ba. Addinin Kirista a Najeriya ba kamar yadda wasu ke tunani bane na kamar ana cin zalin mabiyanta, kulli yaumin karuwa addinin take kuma yawan mabiyanta ya kusa rabin adadin yan Najeriya."

"Hakazalika maganar cewa mabiya addinin Kirista yan Boko Haram sun kaiwa hari; ba dukkan yan matan Chibok ne Kirista ba, wasunsu Musulmai ne, kuma dukkansu yan ta'adda suka sace."

"Maganar gaskiya da ake gani zahiri itace kashi 90% na wadanda Boko Haram ke kaiwa hari Musulmai ne: wannan ya hada da sace dalibai mata Musulmai 100, harbe-harbe cikin Masallaci; da kisan shahrarrun Limamai biyu."

"Abinda kowa ya sani shine wadannan yan ta'addan suna kaiwa marasa galihu hari, masu addini, marasa addini, yara, da manya."

KU KARANTA: Bai taba addinin Musulunci ba ko na sa'a daya - Mahaifin Nathaniel Samuel

Mun kawo muku rahoton wani matashi kirista mai suna Abraham Amuta wanda mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta yi garkuwa dashi tsawon watanni 10 ya watsa ma masu kokarin ceto shi kasa a ido, inda ya bayyana musu ya gwammace ya cigaba da zama da yan ta’addan Boko Haram.

Daily Trust ta ruwaito Boko Haram ta kama Amuta ne a ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2019 yayin da yake aikin yi ma kasa hidima, NYSC, a jahar Borno, inda a ranar Lahadi, 2 ga watan Feburairu ya ki amincewa da tayin da Boko Haram ta masa na komawa gida.

Bayan doguwar tattaunawa, Amuta ya bayyana ma mutanen da suka shiga har cikin dajin Sambisa da nufin amso shi daga hannun Boko Haram cewa shi fa ba zai koma gida ba, domin kuwa ya sauya addininsa, ya fita daga addinin Kiristanci.

Amuta dan asalin jahar Benuwe ya fada hannun Boko Haram ne a lokacin da suka kai wani samame a hanyar Gwoza zuwa Maiduguri yayin da suka nufi garin Chibok don kai ma jama’an garin kayan agaji. Sauran mutanen da yan ta’addan suka sata sun hada da Moses Oyeleke da Ndagliya Ibrahim Umar.

Sai dai bayan watanni bakwai a hannun yan ta’addan, Boko Haram ta saki Fasto Oyelek a watan Nuwambar shekarar 2019, kuma majiyar Legit.ng ta bayyana cewa an cigaba da tattaunawar sako sauran mutanen har sai lokacin da Amuta yace ba zai koma gida ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel