Turai Yar'adua ta ziyarci Aisha Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Turai Yar'adua ta ziyarci Aisha Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta karbaTurai Yar’adua a fadar shuagaban kasa da ke Aso Rock

- Matan biyu sun zagaya gidan gwamnatin tare da ‘ya’aym Taura, Zainab Dakingari da Abdulaziz Yar’adua

- A haduwar tasu, sun samu damar tattauanawa a kan cin zarafin da ake wa jinsi da kuma hanyoyin habaka matasa

An ga hotunan uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Turai Yar’adua, matar tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua. An ga hotunan matan ne suna cikin nishadi.

Aisha Buhari ta wallafa hotunansu ne shafinta na Instagram. Ta bayyana cewa matar tsohon shugaban kasan ta kai mata ziyara ne tare da ‘ya’yanta biyu, Zainab Dakingari da Abdulaziz Yar’adua.

Kamar yadda uwargidan shugaban kasar ta bayyana, ta samu tattauna manyan lamurra da Turai. Ta ce sun tattauna a kan cin zarafin da ya danganci jinsi da kuma hanyoyin habaka matasa a Najeriya.

DUBA WANNAN: An kama likitan bogi da ya yi sanadin rasuwar yarinyar 'yar shekaru uku a Nasarawa

A hotunan, an ga matan biyu suna zagaya fadar shugaban kasar. An hango su suna duba wani bango na matan tsofaffin shugabannin kasa.

Aisha Buhari ta ce Turai ta tuna lokacin da take rayuwa a gidan gwamnatin. Ta jaddada cewa Turai ce ta kirkiro dakin taron matan tsofaffin shugabannin kasa a lokacin da take matar shugaban kasa.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram, “A jiya ne na karba bakuncin ‘yar uwata Hajiya Turai Yar’adua a gidan gwamnati tare da diyarta Zainab Dakingari da danta Abdulaziz Yar’adua. Nayi farin cikin ganinsu kuma mun tattauna abubuwa masu tarin yawa da suka danganci cin zarafin jinsi da kuma hanyar habaka matasan Najeriya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164