'Na san tsohon gwamnan da yake da tawagar kwararrun masu kisa' - Femi Fala, SAN
Babban lauya mai rajin kare hakkin bil adama, Mista Femi Falana, ya bayyana cewa ya san wani tsohon gwamna da ya mallaki tawagar kwararrun masu kisa a daya daga cikin jihohin yankin kudu maso yamma.
Da yake magana a wurin wani taro a jami'ar Ibadan ranar Litinin, Falana ya bayyana cewa tawagar masu kisan tana karkashin kulawar babban jami'in dan sandan da ke aiki tare da gwamnan a wancan lokacin.
Falana ya kara da cewa daga cikin irin mutanen da tawagar kisan ta hallaka akwai wani kwararren ma'aikacin bankin duniya. Amma, bai bayyana sunan tsohon gwamnan ba.
Babban lauyan ya ce daga cikin fargabar da jama'a ke yi a kan bawa jihohi iznin kirkirar 'yan sanda nasu na kansu, shine tunanin cewa zasu mayar dasu karnukan farautar abokan hamayyarsu.
Kazalika, ya kara da cewa kirkirar 'yan sandan jiha ne kadai hanyar da Najeriya zata iya shawo kan matsalolin tsaro da kullum ke kara ta'azzara.
Falana ya furta wadannan kalamai ne yayin da yake gabatar da lakca a wurin taron karrama marigayi Farfesa Olumuyiwa Awe wanda aka yi a dakin taro na 'Trenchard Hall' a jami'ar Ibadan.
A cigaba da tattauna wa a kan matsalolin tsaro a sassan kasa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
Shugaban kasar ya gana da shugabannin majalisar kasar nan ne a ranar Litinin cikin fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.
A yayin bayani ga manema labaran gidan gwamnati jim kadan bayan kammala ganawarsu, Gbajabiamila ya ce shugabannin majalisar ne suka ziyarci shugaban kasa domin samun bayanai dalla-dalla a kan halin da kasar nan ke ciki ta fuskar tsaro.
DUBA WANNAN: Buhari ya aika wa Nanono takardar neman ya kare kansa a kan wata harkallar takin noma
Kamar yadda Gbajabiamila ya sanar, shugaban kasar ya nuna musu damuwarsa a kan halin rashin tsaro da ke addabar kasar nan.
Kakakin majalisar ya bayyana cewa, zancen sauke shugabannin tsaron kasar nan na cikin abubuwan da suka tattauna.
Amma kuma, ya ce har yanzu dai ba a cimma matsaya ba don kuwa akwai mabanbantan ra'ayi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng