Matasan APC sun sha alwashin tona asirin 'yan majalisan da ke neman hambarar da Buhari

Matasan APC sun sha alwashin tona asirin 'yan majalisan da ke neman hambarar da Buhari

- Ana zargin wasu 'yan jam'iyyar All progressives Congress, APC, da shirya makirci domin ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya muzanta

- Kungiyar matasan jam'iyyar APC ne suka bayyana hakan a ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu

- Kungiyar ta ce wadanan 'yan siyasan suna amfani da wasu 'yan majalisa ne suna neman Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus

Kungiyar matasa ta jam'iyyar All Progressives Congress Progressive (APC) mai mulki ta ce za ta bayyana sunayen 'yan majalisa na jam'iyyar da ke kitsa makircin kiraye-kirayen Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus.

A yayin taron manema labarai da ta kira a ranar Juma'a 3 ga watan Fabrairu a Abuja, kungiyar ta ce wasu 'yan jam'iyyar APC ne suka fakewa da wasu suna neman shugaban kasa ya yi murabus.

Sanarwar da shugaban kungiyar, Sanusi Sheriff ya fitar ta ce bangaren matasa na jam'iyyar ta APC tana gargadin wadanda ke raba wa 'yan majalisa kudi domin su hambarar da Shugaba Muhammadu Buhari su shiga taitayin su.

Kungiyar APC ta sha alwashin tona asirin 'yan majalisan da ke neman hambarar da Buhari
Kungiyar APC ta sha alwashin tona asirin 'yan majalisan da ke neman hambarar da Buhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An gano ma'aikatan bogi 60,000 da tsarin IPPIS - Pantami

Sheriff ya ce wasu 'yan siyasa ne masu son tayar da zaune tsaye ke amfani da 'yan majalisar tarayya domin ganin sun samu kujerar mataimakin shugaban kasa nan ba da dadewa ba.

Matasan na APC sun nuna bacin ransu kan yadd wasu 'yan jam'iyyar ta APC ke juya wa shugaba Buhari da jam'iyyar su baya a maimakon girmama jam'iyyar.

Sun ce abin takaici ne yadda shugabanin majalisa suka bari irin wannan abun ya faru tun farko.

A cewar kungiyar, nasarorin da shugaba Muhammadu Buhari ya samu kadai sun isa su wanke shi kuma babu wani sharri da zai saka a hambarar da shi.

Kungiyar ta kuma shawarci shugabanin majalisar tarayya da kada su bari ayi amfani da su wurin tayar da zaune tsaya a Najeriya.

Ya ce wadanda ke kitsa wannan makircin burinsu kawai shine ganin an tsige shugaba Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel