Lakabin 'matar aure' ga 'ya mace ya fi gwamnan CBN daraja - Adamu Garba

Lakabin 'matar aure' ga 'ya mace ya fi gwamnan CBN daraja - Adamu Garba

- Wani dan Najeriya ya wallafa rubutu a dandalin sada zumunta kan auren mata biyu da irin suka da mutane ke yi wa masu auren mata biyu

- A cewarsa, lakabin 'matar aure' ga 'ya mace ya fi daraja a kan lakabin gwamnan babban bankin Najeriya CBN

- Mutane da dama a dandalin sada zumunta sun bayyana ra'ayoyinsu a kan batun

Wani dan kasuwa a Najeriya ta wallafa rubutu a shafin sada zumunta yana kare auren mata biyu a yayin da mutane ke tafka muhawarra a kan lamarin. Mutumin mai suna Adamu Garba ya wallafa sakonsa ne ga mata da ba su riga sunyi aure ba.

Garba wanda ke da dimbin magoya baya a Twitter ya kwatanta lakabin matan aure da gwamnan babban bankin Najeriya CBN. A cewarsa, yin aure ya fi muhammaci da zama gwamnan CBN nesa ba kusa ba.

Ya rubuta: "Ban san dalilin da yasa ra'ayi na a kan auren mata da yawa ke damun gwaurayen mata ba. A ra'ayi na, kuna bari babban garabasa yana wuce ku. Bari in fada muku, ki samu a rika kiran ki da labakin 'Matar aure' ya fi muhimmanci a gare ki da zama gwamnan CBN."

DUBA WANNAN: An gano ma'aikatan bogi 60,000 da tsarin IPPIS - Pantami

Sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta ya janyo hankulan mutane sosai, galibin cikinsu ba su yarda da ra'ayinsa ba inda wasu ke zarginsa da amfani da batun kawai domin ya yi suna.

Akwai wani mai amfani da shafin Twitter da ya yi ikirarin cewa yana shaye-shaye kuma cikin maye ya wallafa sakon.

Ga dai wasu daga cikin ra'ayoyin da mutane suka bayyana a kan batun.

@jossynme ta ce: "Shi kuma wannan daga ina ya ke??? Dakikanci!

@Dammyy: "Mene na ke karantawa.

@QdPaper: "Adamu Garba shi dai kullum so ya ke rika tashe a Twitter, saboda mutane su gane irin samfurin haukarsa.

@daisanna91: "Idan shugaba ya sha ganyen wiwi da ta lalace, shi ma ya kan mata cewa ya lalace.

@femirewaju: "Yanzu na fahimci dalilin da yasa mawallafa na kasashen yamma ke kiran Afirka nahiyar jahilai."

Galibin iyaye dai a nahiyar Afirka suna bawa aure muhimmanci sosai kuma suna matukar son su ga yaransu sun samu mazan aure duk da irin matsayin da suka kai a rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel