Fada da cikawa: Gwamnatin jihar Kaduna na bi titi-titi domin damke yaran da basu zuwa makaranta
Bayan barazanar da gwamnatin jihar Kaduna ta yiwa iyayen da suke hana yaransu zuwa makarantun Boko duk da cewa gwamnatin ta mayar kyauta, an fara daukan yaran da aka gani a titi lokacin makaranta.
Hotuna da suka yadu a shafukan Soshiyal Midiya sun nuna jami'an wata sabuwar hukumar a jihar Kaduna da sunan 'Edumarshal' a kan titi daga cikin titunan jihar da yara cikin mota.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
A baya, mun kawo muku rahoton cewa A ranar Juma'a, gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga iyaye su tura yaransu makaranta ko su fuskanci fushin hukumar bisa da dokokin da jihar ta ayyana.
Sakatariyar din-din-din ta ma'aikatar Ilimin jihar, Phoebe Yayi, ta yi wannan kira ne a hirar da tayi da kamfanin dillancin labarai a Kaduna.
Madam Phoebe tace hakkin ko wani yaro ne ya samu ingantaccen ilimin firamare kuma kyauta, saboda haka wajibin gwamnatin jihar ne ta samar da hakan.
Ta ce saboda wajabcin haka aka alanta Ilimi kyauta da dukkan yaran jihar Kaduna daga Firamare zuwa Sakandare a jihar.
Tace: "Saboda haka, iyayen basu da wani uzurin hana yaransu zuwa makaranta tunda gwamnati t dauke musu nauyin dukkan wani nauyi."
"Ya kamata a sani cewa dokar kare yara ta 2018, sashe na 18 (6) ta ayyana cewa duk Uba, Uwa ko waliyyin da ya hana dansa ko diyarsa zuwa makaranta ya aikata laifi."
"Dokar ta cigaba da cewa duk mahaifin da aka kama a karon farko da wannan laifi zai garkama kuma a wajabta masa aikin al'umma ba biya; idan kuma aka sake kamashi karo na biyu, za'a ci sa tara ko kuma a daureshi a Kurkuku."
"Saboda haka tura yara makaranta ya zama wajibi ba zabi ba kuma kin yin hakan na ukubar dauri."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng