Ikon Allah: Harsashi ya kashe ta amma dan cikinta ya rayu

Ikon Allah: Harsashi ya kashe ta amma dan cikinta ya rayu

- Likitocin asibitin Ascension St. Joseph sun samu nasarar cire jariri daga cikin mahaifiyar shi bayan ta rasu

- Wani dan bindiga ne ya harbe mahaifiyar yayin da take cikin wata mota da ke gaban wata mashaya a Milwaukee

- Jami’an ‘yan sandan yankin sun ce basu kama kowa ba har a ranar Lahadi kuma basu da tabbacin ko mai cikin dan bindigar ya hara

Likitocin asibitin Ascension St. Joseph da ke Milwaukee a Amurka sun yi nasarar fitar da jariri daga cikin matacciyar mahaifiyar shi ta hanyar yi mata aikin gaggawa.

Matar mai suna Annie Sandifer tana cikin wata mota ne a gaban mashayar Milwaukee lokacin da wani dan bindoga ya harbo harsasai biyar zuwa shida. Lamarin ya faru ne wajen karfe 2:30 na daren Asabar. Tuni harsashin ya sameta kuma ta fadi matacciya.

Ikon Allah: Harsashi ya kashe ta amma dan cikinta ya rayu
Ikon Allah: Harsashi ya kashe ta amma dan cikinta ya rayu
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa jaririn na lafiya kalau amma an cire shi daga ckin mahaifiyar ne a lokacin da yake da makonni 26. An haifeshi ne bai isa haihuwa ba kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

KU KARANTA: Dalibar da aka kora a makaranta ta mallaki kamfanin biliyan 2 bayan fara sana'a da dubu 164

Jami’an ‘yan sandan a ranar Lahadi sun ce basu kama kowa ba har a lokacin amma kuma basu da tabbacin ko dan bindigar motar da matar ke ciki yayi niyyar hara.

A ranar Asabar ne ‘yan uwan Sandifer suka kwatanta ta da mutum mai matukar kirki kuma uwa ta gari ga yaranta biyar. Sun bayyana cewa Sandifer ta rasu ne tana da shekaru 35 a duniya kamar yadda mujallar Milwaukee Sentinel ta ruwaito.

“Duk wani hakki na uwa tana saukewa. Tana iya bakin kokarinta a kan ’ya’yanta,” cewar dan uwanta mai suna Kisha Ducksworth.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel