Tashin hankali: An kama mutum 3 da suka yiwa dokuna, shanu, akuyoyi da karnuka fyade

Tashin hankali: An kama mutum 3 da suka yiwa dokuna, shanu, akuyoyi da karnuka fyade

- Wasu maza uku a kasar Pennysyilvania an yanke musu hukuncin shekaru 20 zuwa 41 a gidan yari

- An kama su da laifin lalata da sa, akuya da kuma dawakai guda 12 a wani gidan gona da ke kasar

- An gano cewa suna saduwa ne da dawakan mata tun daga shekarar 2014 kuma suna yi ne duk sati

Wasu maza uku masu matsalar rashin lafiya sun shiga hannun jami’an tsaro bayan da aka kama su da laifin cin zarafin dabbobi fiye da sha biyu a cikin shekaru biyar. Mazan uku da aka gano sunansu da Mathew Brubaker mai shekaru 31, Marc Meansnikoff mai shekaru 34 da kuma Terry Wallace mai shekaru 41 an yanke musu hukuncin daga shekaru 20 zuwa 41 a gidan yari ne.

An kama su da laifin lalata da sa guda daya, akuya, dawakai tara da kuma karnukan da ba zasu kirgu ba. Dukkansu an tuhumesu ne da laifuka sama da 1,400 da suka hada da zaluntar dabbobi, lalata da dabbobi da kuma lalata kananan dabbobi.

Tashin hankali: An kama mutum 3 da suka yiwa dokuna, shanu, akuyoyi da karnuka fyade
Tashin hankali: An kama mutum 3 da suka yiwa dokuna, shanu, akuyoyi da karnuka fyade
Asali: Facebook

An gano cewa wani yaro ne ke tsare dabbobin yayin da mazan uku ke lalata dasu. A halin yanzu dai an mika dabbobin hannun Pennsylvania Society for the Prevention of Cruelty to Animals don ci gaba da kula dasu, kamar yadda jaridar Rare animals ta ruwaito.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kungiyar 'yan madigo sun kai karar hukumar CAC gaban kotu a Abuja

An fara kama mazan uku ne a shekarar 2018 bayan da yaron mai shekaru 16 ya sanar da ‘yan sanda yadda suke lalata da dabbobi. An dauke yaron tare da duba lafiyar shi kuma ba a ga wata alama ta ana cin zarafinshi ba.

‘Yan sandan Pennsylvania din sun samu damar binciko gidan gonar inda mazan da yaron ke zama kuma sun samu wasu bidiyo na yadda suke lalata da dabbobin.

Bayan tsananta bincike, jami’an tsaron sun ga wani abu da mazan suka hada ta yadda zasu samu damar lalata da dabbobin. Dan sandan mai gabatar da karar ya ce sun fara cin zarafin dabbobin ne tun a 2014 kuma suna yi ne duk sati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel