An kama likitan bogi da ya yi sanadin rasuwar yarinyar 'yar shekaru uku a Nasarawa

An kama likitan bogi da ya yi sanadin rasuwar yarinyar 'yar shekaru uku a Nasarawa

Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC sun kama wani mutum da ake zargin ya dade yana aiki a matsayin likitan bogi a jihar Nasarawa.

Wanda ake zargin mai suna Mudassir Mohammed Idris ya kwashe kimanin shekaru biyu yana aiki kafin asirinsa ya tonu bayan wata yarinya mai shekaru 3, Hauwa ta rasu sakamakon karin jini da aka yi mata a asibitinsa.

Da ya ke zanta wa da manema labarai, kwamandan NSCDC Mahmoud Gidado Fari ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan mahaifin yarinyar da ta rasu ya shigar wa jami'an tsaron rahoto.

"Mun kama likitan bogin, za mu gurfanar da shi a gaban kotu kan kisar gillar da ya yi wa yarinyarn domin ya yi wa yarinya mai shekaru uku karin jini ba bisa ka'ida ba wadda hakan ya yi sanadiyar mutuwar ta nan take," in ji shi.

An kama likitan bogi kan rasuwar wata yarinya 'yar shekara 3 a Nasarawa
An kama likitan bogi kan rasuwar wata yarinya 'yar shekara 3 a Nasarawa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An gano ma'aikatan bogi 60,000 da tsarin IPPIS - Pantami

Mudassir da ya nemi ayi masa afuwa ya ce ya yi wa wasu marasa lafiyan karin jini a baya kafin Hauwa, inda ya ce shi dalibi ne a Kwallejin Kimiyar Lafiya ta Gboko a jihar Benue.

An kuma gano cewa yana da wani shagon sayar da magunguna mara rajista kuma ya kwashe kimanin shekaru biyu yana aiki a matsayin likita ba tare da lasisi ba ko satifiket na lititanci.

A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoton wani likitan bogi da shima asirinsa ya tonu a jihar Kano.

Hukumar kula da lafiya na jihar Kano (PHIMA) da ke karkashin ma'aikatan lafiya ta kasa tare da hadin gwiwar kungiyar likitocin Najeriya NMA ne suka kai wata sumame kuma suka kama mutumin mai suna Ibrahim Adamu.

Adamu ya dade yana ikirarin cewa shi kwararren likita ne mai lasisin aiki kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Da ya ke magana da manema labarai jim kadan bayan kamen, sakataren PHIMA, Dakta Usma Tijjani Aliyu ya ce sun dade suna bibiyan wanda ake zargin.

Ya ce an kama Adamu ne bayan sun samun rahoton cewa yana yawo a asibitocin jihar har ma da asibitocin jihohin da ke makwabtaka da Kano.

Dakta Usman ya ce wanda ake zargin yana hannun 'yan sanda suna cigaba da bincike a halin yanzu.

Ya ce wanda ake zargin ya tabbatar da zargin da ake masa inda ya ce yana aiki ne da takardun wani likitan da ya sace ba tare da saninsa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel