Mutuwa riga: Dan majalisar wakilai daga Katsina ya rasa matarsa a Abuja

Mutuwa riga: Dan majalisar wakilai daga Katsina ya rasa matarsa a Abuja

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Batagarawa/Charanchi/Rimi a majalisar wakilan Najeriya, Alhaji Hamza Dalhatu ya rasa matarsa a wani mummunan hadarin mota da ya auku a babban birnin tarayya Abuja.

Katsina Post ta ruwaito wannan hadari ya faru ne da yammacin Lahadi, 2 ga watan Feburairu, yayin da matar dan majalisar mai suna Hajiyar Maryam ta rasu a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairun shekarar 2020.

KU KARANTA: Tabarbarewar tsaro: Gwamnati za ta yi daukan sabbin Sojoji na gaggawa – Osinbajo

Wata majiya ta karkashin kasa ta shaida ma majiyarmu cewa an yi kokarin ceto rayuwar Hajiya Maryam ta hanyar garzayawa da ita zuwa wani Asibiti dake garin Abuja, amma koda aka isa ta fita cikin hayyacinta, daga bisani kuma aka sanar da mutuwar ta ta.

Daga karshe majiyar ta tabbatar da cewa tuni an yi mara jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Hajiya Maimuna ta mutu ta bar mijinta da yara 5, dsa fatan Allah Ya jikanta da gafara, Amin.

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai shirin daukan sabbin zaratan Sojoji nan bada jimawa ba a kokarin gwamnatin Najeriya na kara adadin jami’an tsaro domin su kawar da matsalar tsaro a kasar.

Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairu yayin da ya karbi bakoncin wasu Fastoci a karkashin kungiyar fastocin yankin Arewacin Najeriya masu rajin kawo zaman lafiya a yankin.

Osinbajo ya bayyana cewa: “Muna yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen matsalar tsaro, muna tafiyar da tsaron nan yadda ya kamata, daga ciki har da aika Sojoji bakin daga domin yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

“Har ma a yanzu zamu kara daukan sabbin Sojoji a rundunar Sojan kasa, kuma zamu dauke su ne a tsarin gaggawa, kuma zamu sayi karin makamai da sauran kayan aiki. A zaman karshe da muka yi na majalisar tsaro mun tattauna yiwuwar kara yawan Sojoji.

“Mun tattauna yadda zamu hada kai da matasa jarumai yan sa kai da sauran yan banga, don haka muna aiki tukuru wajen tsaurara matakan tsaro, musamman yadda zamu yi amfani da na’ura wajen leken asiri a kasar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel