Za a dawo da binciken jaka a kasuwanni, tasha, makarantu da wuraren bauta a Kaduna

Za a dawo da binciken jaka a kasuwanni, tasha, makarantu da wuraren bauta a Kaduna

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta shawarci makarantu, wuraren bauta, kasuwanni, tashar motoci da sauran wuraren da jama'a ke taruwa da su dawo da salon duba kayan mutane kafin barinsu shiga.

Wannan shawarar ta biyo bayan kama wani mutum da ake zargin dan kunar bakin wake mai suna Nathaniel Samuel, a cocin Living Faith da ke Sabon Tasha Kaduna, a ranar Lahadi.

An kama wanda ake zargin ne yayin da ya shige cikin masu bauta tare da wani abu mai fashewa a cikin jakarsa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo, a wata tattaunawa da manema labarai da yayi, ya ce a dau matakan da suka dace don gudun karantsaye ga tsaron jihar.

DUBA WANNAN: An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Umar Muri yayi umarni ga jami'an tsaro da su tsananta sa ido tare da hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a jihar don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

Ya tabbatarwa jama'ar jihar cewa za a ci gaba da samar da tsaro ta hanyar daukar duk matakan da suka dace a jihar.

A jiya ne rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana bayanai a kan mutumin da aka kama da bam a cocin Living Faith da ke Sabon Tasha a yankin karamar hukumar Chikun ta jihar.

An bayyana sunansa da Nathaniel Samuel, mutum mai matsakaicin shekaru wanda 'yan sandan suka mika ga sashin binciken manyan laifuka don amsa tambayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel