Bayan shekaru 50, an bude Masallaci a kasar Sloveniya

Bayan shekaru 50, an bude Masallaci a kasar Sloveniya

An bude Masallacin kasar Slovenia ta farko a babbar birnin jihar, Ljubljana, a ranar Litinin bayan shekaru 50 da neman izinin ginin da kuma rikice-rikice da yan adawan Musulunci yan siyasar kasar.

Shugaban al'ummar Musulman kasar Mufti Nedzad Grabus yace bude wannan Masallaci babban sauyi ne a rayuwarsu.

Yace: "Slovenia ce kasar da ta fito da Yugoslav ta karshe da zata samu Masallaci."

Shekaru 50 da suka gabata, Musulman kasar sun nemi izinin gina Masallaci lokacin da take Yugoslavia.

Sai shekaru 15 da suka gabata aka bada izinin ginawa, amma kuma aka fara fuskantan adawa daga yan siyasa dake adawa da Musulunci da Musulmai.

Bayan shekaru 50, an bude Masallaci a kasar Sloveniya
Bayan shekaru 50, an bude Masallaci a kasar Sloveniya
Asali: Facebook

A cewar Mufti Grabus, an fara ginin a shekarar 2013, kuma na kashe $39 million kuma kasar Qatar ce ta bada gudunmuwar $33 million.

An gina Masallacin a babbar birnin kasar kuma za ta iya daukan yawan mutane 1400. Hakazalika akwai ofishoshi, makaranta, dakin karatu, dakin cin abinci, wajen kwasan kwallon kwando, gidajen malamai da dogon Hatsumiya a Masallacin.

Gabanin yanzu, Musulman kasar suna ibada da tarurrrukansu a dakunan haya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel