Motar 'yan sanda ta kife yayin tsere da wata motar haya, biyu sun mutu nan take

Motar 'yan sanda ta kife yayin tsere da wata motar haya, biyu sun mutu nan take

Wasu jami'an 'yan sanda biyu sun mutu bayan motar da suke ciki ta kife yayin da suka bi wata motar haya.

Jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Ogoni zuwa Akwa Ibom yayin da motar 'yan sandan ta biyo wata motar fasinja kirar 'Sienna' domin tsayar da ita.

A garin gudun bin motar ne sai motar jami'an 'yan sanda ta kwace, inda ta hantsila, ta fada cikin wani rami dake gefen hanya.

Jami'an 'yan sanda biyu sun mutu nan take, shi kuma direban motar hayar ya tsere.

Motar 'yan sanda ta kife yayin tsere da wata motar haya, biyu sun mutu nan take
Motar 'yan sanda ta kife yayin tsere da wata motar haya
Asali: Twitter

Ya zuwa yanzu rundunar 'yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa ko jawabi danagane da hatsarin da ya ritsa da jami'anta ba.

A wani labari da Legit.ng ta wallafa ranar Lahadi, an kwantar da tsohon minitsan wasanni da matasa, Barista Solomon Dalung, a wani asibitin birnin tarayya, Abuja, bayan ya kamu da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.

DUBA WANNAN: Abubuwa 5 da ke fitar da soyayyar namiji daga zuciyar mace

"Ina neman addu'arku, an kwantar da ni a asibiti", kamar yadda tsohon ministan ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta (Facebook) ranar Asabar. Amma, bai bayyana irin larurar da yake fama da ita ba.

Sakon na Dalung ya yi farin jini a wurin jama'a, inda suke tofa albarkacin bakinsu tare da bayyana mabanbantan ra'ayoyi.

Wasu manema labarai sun kira lambar tsohon ministan domin neman karin bayani daga gare shi amma bai samu damar amsa kiransu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel