Saboda tsananin rashin tsaro, jirgin sama ta kaddamar da daukan fasinjojin Abuja-Kaduna

Saboda tsananin rashin tsaro, jirgin sama ta kaddamar da daukan fasinjojin Abuja-Kaduna

Wata kamfanin jiragen sama ta kaddamar da daukan fasinjoji daga birnin tarayya Abuja zuwa Kaduna saboda tsananin rashin tsaron da ya addabi mutane a hanyar mota da kuma jirgin kasa.

Kamfanin Misha Travles ta kaddamar da shirin ne a ranar Litin da taken "Babu Gajiya, Babu tsoro'.

Wannan shine karo na farko da jirgin sama zatayi sufurin jama'a a tafiya mai gajeren lokaci irin wannan.

Saboda tsananin rashin tsaro, jirgin sama ta kaddamar da daukan fasinjojin Abuja-Kaduna
Saboda tsananin rashin tsaro, jirgin sama ta kaddamar da daukan fasinjojin Abuja-Kaduna
Asali: Twitter

Wani ma'aikacin kamfanin Misha Travles, Tope Popoola, ya bayyana cewa lallai tsawon tafiyan yayi kadan amma saboda tsananin rashin tsaron hanyar, da alamun za'a samu kasuwa.

Yace: "Mun lura sosai da yadda rashin tsaro ya addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja, kuma mun ga akwai kasuwa."

"Yawancin mutane zasu ga sunfi sabawa da tuka motar awa biyu ba nisa. Amma mutane sun fi damuwa da lafiyarsu."

Kamfanin jirgin na amfani da jirgin Bombadier CRJ da ka iya daukan mutane 50 a lokaci guda.

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin jahar Kaduna ta tsaurara matakan tsaro a yankin tashar jirgin kasa dake unguwar Rigasa a jahar Kaduna domin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji da dukiyoyinsu.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a lokacin daya kai ziyara tashar jirgin kasa na Rigasa a ranar Litinin domin auna matsayin tsaro a yankin.

Sabbin tsare tsaren tsaro da gwamnatin ta dauka ya biyo bayan jita jitan da ake yawan samu na masu garkuwa da mutane dake kai hare hare a kan fasinjojin da suka fita daga tashar jirgin ko kuma suke kan hanyar zuwa tashar jirgin.

Kwamishina Aruwan yace sun girke tawagar hadakan jami’an tsaro daga rundunar Soja, Yansanda, Civil Defence da sauran hukumomin tsaro a tashar da yankunan dake makwabtaka da ita, haka zalika za su dinga gudanar da sintiri a yankin gaba daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel