Gwamna El-Rufai ya kara karfafa tsaro a tashar jirgin kasa dake Rigasa Kaduna

Gwamna El-Rufai ya kara karfafa tsaro a tashar jirgin kasa dake Rigasa Kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna ta tsaurara matakan tsaro a yankin tashar jirgin kasa dake unguwar Rigasa a jahar Kaduna domin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji da dukiyoyinsu.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a lokacin daya kai ziyara tashar jirgin kasa na Rigasa a ranar Litinin domin auna matsayin tsaro a yankin.

Gwamna El-Rufai ya kara karfafa tsaro a tashar jirgin kasa dake Rigasa Kaduna
Tashar jirgin kasa Rigasa Kaduna
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da Mata da Miji a babban birnin tarayya Abuja

Sabbin tsare tsaren tsaro da gwamnatin ta dauka ya biyo bayan jita jitan da ake yawan samu na masu garkuwa da mutane dake kai hare hare a kan fasinjojin da suka fita daga tashar jirgin ko kuma suke kan hanyar zuwa tashar jirgin.

Kwamishina Aruwan yace sun girke tawagar hadakan jami’an tsaro daga rundunar Soja, Yansanda, Civil Defence da sauran hukumomin tsaro a tashar da yankunan dake makwabtaka da ita, haka zalika za su dinga gudanar da sintiri a yankin gaba daya.

A jiya ne rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna ta sanar da kama wani matashi mai matsakaicin shekaru da ya yi kokarin dasa bom a cikin wani cocin dake unguwar sabon tasha, cikin karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna.

Mai magana da yawun Yansandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya bayyana a ranar Lahadi inda ya bayyana sunan matashin a matsayin Nathaniel Samuel, wanda yace masu gadin cocin Living Faith Church ne suka kama shi dake da Bom a cikin jaka

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga dadi sun yi garkuwa da wani mutumi mai suna Abdullahi Otto tare da matarsa mai dauke da juna biyu, Maimuna Abdullahi daga gidansu dake babban birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya auku ne a ranar Asabar, 1 ga watan Feburairu a gidan ma’auratan dake unguwar Kekeshi dake cikin karamar hukumar Abaji na Abuja, kamar yadda wani dan uwan Abdullahi daya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar.

Majiyar ta kara da cewa dan uwan Abdullahi yace da misalin karfe 10:34 na daren Asabar ne yan bindigan da adadinsu ke da yawa suka kutsa kai gidan ma’auratan dauke da muggan makamai suna harbe harbe a sama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel