Yaki da ta’addanci: Boko Haram sun kashe zaratan Sojoji 3, sun kwace motocin yaki 2

Yaki da ta’addanci: Boko Haram sun kashe zaratan Sojoji 3, sun kwace motocin yaki 2

Kungiyar Boko Haram dake biyayya ga kungiyar ta’addanci ta duniya, ISIS, watau ISWAP ta kashe wasu zaratan dakarun Sojin Najeriya guda uku tare da kwace motocin yaki guda biyu a wani hari da suka kai ma Sojoji a ranar Juma’a.

Jaridar Punch ta ruwaito mazauna garin Askira sun bayyana cewa yan ta’addan sun dira garin ne da tsakar daren Juma’a a cikin wasu motocin a kori kura guda biyu da suka daura ma bindigu tare da alburusai, inda suka yi ta fafatawa da Sojoji da matasa yan sa kai a garin.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da Mata da Miji a babban birnin tarayya Abuja

Wani jami’in Soja da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Sojojinmu sun fatattaki yan Boko Haram, amma sun kashe mana Sojoji uku, kuma sun tafi da motocin yakinmu guda biyu, sai dai mu ma mun kashe musu mayaka da dama.”

Shi ma wani dan sa kai, Adamu Galadima ya bayyana cewa bayan samun labarin yan ta’adda sun nufo garin, sun shirya musu kwantan bauna; “An yi gumurzu sosai, wanda yasa dole suka ranta ana kare, amma Sojoji uku sun mutu, sai kuma yan gari guda 5 da suka samu rauni.”

Shi ma wani dan sa kai mai suna Peter Malgwui yace bayan mayakan Boko Haram sun tsere daga Askira, sun tsaya a wani kauyen Kilangar dake kimanin kilomita 15 daga Askira, inda suka kai ma wani asibiti hari suka kwashe magunguna.

Ko a ranar Lahadi, sai da kungiyar ISWAP ta fitar da sanarwar kashe Sojoji 7 tare da kwace motocin yaki 3 daga wannan hari da ta kai garin Askira. A shekarar 2016 ne ISWAP ta balle daga shugabancin Shekau a Boko Haram, kuma ta mayar da hankalinta wajen kai ma Sojoji da sansanoninsu hari.

Shi ma garin Askira Uba ya sha fama da hare haren ta’addanci sakamakon kasancewarsa kusa da dajin Sambisa, wanda shi ne babban mafakar mayakan ta’addanci a gaba daya yankin Arewa maso gabas.

A wani labarin kuma, wani matashi kirista mai suna Abraham Amuta wanda mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta yi garkuwa dashi tsawon watanni 10 ya watsa ma masu kokarin ceto shi kasa a ido, inda ya bayyana musu ya gwammace ya cigaba da zama da yan ta’addan Boko Haram.

Boko Haram ta kama Amuta ne a ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2019 yayin da yake aikin yi ma kasa hidima, NYSC, a jahar Borno, inda a ranar Lahadi, 2 ga watan Feburairu ya ki amincewa da tayin da Boko Haram ta masa na komawa gida.

Bayan doguwar tattaunawa, Amuta ya bayyana ma mutanen da suka shiga har cikin dajin Sambisa da nufin amso shi daga hannun Boko Haram cewa shi fa ba zai koma gida ba, domin kuwa ya sauya addininsa, ya fita daga addinin Kiristanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel