Kotu ta yankewa yan fashi biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jos

Kotu ta yankewa yan fashi biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jos

Wata babbar kotu dake Jos a ranar Litinin ta yankewa wasu matasa biyu, Dayabu Ahmad 20, da Umar Aliyu, 21, hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin fashi da makami.

Alkali S.P Gang ya kama su da laifin fashi da muggan makami inda suka tare hanyar Barkin Ladi/Mangu suka kwacewa matafiya dukiyoyinsu.

Yace: "Wannan hukunci ya zama dole saboda doka ta tanadi cewa duk wanda aka kama da laifin fashi da makami a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya."

"Wannan kotu ta yanke ma kai, Dayabu Ahmad da Umar Aliyu, hukuncin rataya har sai kun mutu. Allah ya jikanku."

Kotu ta yankewa yan fashi biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jos
Kotu ta yankewa yan fashi biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jos
Asali: Twitter

An gurfanar da su ne ranar 19 ga Febrairu 2019. A jawabin da suka yi, sun amince da aikata laifin kuma sun ce sharrin shaidan ne, da kuma halin rashin kudi.

Abubuwan da suka kwata sun hada da; kilon nama 1, galan man gyada 1, kwalin Maggi 1, kankana da N100,000.

Alkalin matasan, Thimas Ochigbo, ya ce zai karbi takardar shari'ar domin ganin yadda za su daukaka karar wannan hukunci.

Za ku tuna cewa a ranar 27 ga Junairu, Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja dake unguwar Maitama ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa kan laifin kisan mijinta Bilyaminu Bello.

Kotun ta kama Maryam da laifin kashe mijinta kuma an tabbatar da dukkan tuhume-tuhumen da ake mata. Za'a ajiyeta a gidan kurkukun Suleja har ta gama daukaka kara.

An gurfanar da ita ne kan zargin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda yake dan'uwan tsohon shugaban PDP, Alhaji Bello Halliru Muhammada 2017.

An gurfanar da ita tare da dan 'uwanta, Aliyu Sanda; mahaifiyarta, Maimuna Aliyu, da mai aikin gidanta, Sadiya Aminu, wadanda ake tuhuma da kokarin boye gaskiya ta hanyar goge jinin marigayin bayan kisansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel