Rashin tsaro: Akalla mutane 245 aka kashe a watan Junairu (Duba jerin wadanda aka kashe)

Rashin tsaro: Akalla mutane 245 aka kashe a watan Junairu (Duba jerin wadanda aka kashe)

Akalla mutane 245 suka rasa rayukansu a watan farkon shekarar 2020, rahotannin kashe-kashe da aka tattara ya bayyana hakan.

A cewar rahoton bincike da InterNations ta gudanar, Najeriya ce kasa mafi hadarin zama a duniya na uku bayan kasar Afghanistan da Syriya.

Ga jerin yadda kashe -kashen suka auku a watan Junairu:

2 ga Junairu: Sojojin Najeriya sun kashe yan Boko Haram 8 yayinda sukayi kokarin kai hari Michika, jihar Adamawa

4 ga Junairu: Wasu yan bindiga sun hallaka mutane 23 a garin Tawari, a jihar Kogi

6 ga Junairu: Akalla mutane 30 suka hallaka yayinda Bam ta tashi da su kan gada a Gamboru, jihar Borno

Hakazalika a ranar, an hallaka jami'an Sojin ruwa hudu yayinda akayi garkuwa da turawa uku a Neja Delta.

Kuma dai a ranar, an hallaka Sojoji hudu a kauyen Gwarm, karamar hukumar Munya ta jihar Neja.

7 ga Junairu: Wani dan sanda a Yenegoa, jihar Bayelsa ya hallaka mutane uku: Direba, mai bautan kasa, da wani mutum daya.

Hakazalika a ranar, fusatattun matasa sun babbaka wasu barayi biyu da suka kai hari shagon aski yayinda wasu bindiga kuma suna kashe wani Yasir Umar a jihar Katsina.

9 ga Junairu: Hukumar yan sandan jihar Plateau ta tabbatar da kisan mutane 12 a kauyen Kulben, karamar hukumar Mangu ta jihar.

11 ga Junairu: Yan bindgia sun bindige jami'an Sojin sama hudu a hanyar Birnin Gwari, jihar Kaduna.

14 ga Junairu: Rikici tsakanin manoma da makiyaya ya haddasa kisan mutane biyu a garin Sobe, karamar hukumar Owan ta jihar Edo.

Hakazalika a ranar, an hallaka Sojin ruwa 4 a kauyen Gbagira, karamar hukumar Ilaje ta jihar Ondo.

16 ga Junairu: Wasu yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara inda suka hallaka akalla mutane 23.

A ranar kuma, yan bindiga suka kaiwa sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, harin kwantan bauna a hanyar Kaduna zuwa Zariya inda suka kashe akalla mutane 6.

18 ga Junairu: An hallaka Soja daya da Boko Haram hudu a musayar wutan da akayi a Ngala, yayinda aka kashe yan gudun hijra akalla 20.

Hakazalika ranar yan Boko Haram suka kashe Sojoji 4 a Bama.

A ranar dai, rikicin kabila ya barke a karamar hukumar Igalamela-Odolu a jihar Kogi kuma akalla mutane 4 sun hallaka.

19 ga Junairu: Gobara ta hallaka mutane biyar yayinda Barayin mai suka fasa bututu mai a jihar Legas

Hakazalika a ranar, bidiyo ya bayyana inda wani dan karamin yaro na Boko Haram ya kashe wani dalibi

20 ga Junairu: An hallaka akalla Sojoji 17 yayinda akayi garkuwa da dama cikinsu a artabun da ya auku tsakanin Soji da Boko Haram kan hanyar Bama-Gwoza.

21 ga Junairu: An hallaka Sojoji 8 a musayar wuta da Boko Haram a Kaga, jihar Borno.

Yan bindiga sun hallaka mutane 4 a karamar hukumar Keana a jihar Nasarawa, yan Boko Haram sun hallaka shugaban CAN, Lawal Andimi, kuma yan bindiga suka kashe muyane 14 a Batsari jihar Katsina.

23 ga Junairu: Yan Boko Haram sun hallaka mutane 10 a Dikwa.

24 ga Junairu: Fusatattun matasa sun hallaka barayi biyu a karamar hukumar Yenagoa, jihar Bayesla.

25 ga Junairu: Yan kunar bakin wake sun tayar da Bam a Masallaci a garin Gwoza, jihar Borno. Mutane 3 suka hallaka yayinda da yawa suka jikkata.

Hakazalika a ranar, yan bindiga sun hallaka mutane mutane 13 a Kwatas, karamar hukumar Bokkos jihar Plateau yayinda yan bindiga suka kashe mutane 11 a jihar Neja.

27 a Junairu: Wani matashi ya burmawa budurwarsa wuka har lahira saboda ta amsa wayan wani saurayi

29 ga watan Junairu: Wani mutum mai suna Kalu ilum ya bindige matarsa, a Etitiama Nkporo dake Ohafia jihar Abia. Sai matasan gari suka banka masa wuta.

Hakazalika wasu makiyaya sun kashe muaten 2 a karamar hukumar Ovia ta Arewa a jihar Edo.

30 ga Junairu: Yanfashi sun hallaka wani dan bautan kasa, Adebayo Mukaila, a jihar Osun

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel