Da duminsa: An damke dan kunar bakin wake da yaje Coci tayar da Bam a Kaduna

Da duminsa: An damke dan kunar bakin wake da yaje Coci tayar da Bam a Kaduna

A ranar Lahadi, hukumar yan sandan sun kawar da wani harin Bam da wani da kunar bakin wake ya kai cocin Living Faith Church, aka Winners Chapel dake Unguwar Sabon Tasha, jihar Kaduna.

A cewar TNG, an damke matashin ne da kayayyakin hada Bam a cikin cocin.

An tattaro cewa wannan ba shi bane karo na farko da matashin zai kai ziyara cocin ba; majiya ta bayyana cewa ko makon da ya gabata ya kai ziyara cocin amma aka hanashi shiga.

Wani majiya a cocin, Ekpenyong Edet, wanda yayi ikirarin cewa shine shugaban jami'an tsaron cocin ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Da duminsa: An damke dan kunar bakin wake da yaje tayar da Bam Coci a Kaduna
Da duminsa: An damke dan kunar bakin wake da yaje tayar da Bam Coci a Kaduna
Asali: UGC

Da duminsa: An damke dan kunar bakin wake da yaje Coci tayar da Bam a Kaduna
Da duminsa: An damke dan kunar bakin wake da yaje Coci tayar da Bam a Kaduna
Asali: Facebook

Edet ya bayyana cewa an ga dan kunar bakin waken ta na'urar CCTV dauke da jaka yayinda ya shiga cikin Coci. Ya samu nasarar shiga har ya zauna kafin aka duba jakansa, aka gano Bam ciki.

Ya ce an mikashi ga yan sanda kuma an kai ofishin hukumar dake Sabon Tasha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel