Kurunkus: Dukkan yan majalisar dokokin Imo sun koma APC, illa mutum 1

Kurunkus: Dukkan yan majalisar dokokin Imo sun koma APC, illa mutum 1

Kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Chiji Collins a ranar Asbar ya bayyana cewa yan majalisar dokokin jihar 26 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Daga cikin yan majalisan dokokin jihar 27, tsohon mataimakin kakakin, Okey Onyekanma, ne kadai ya rage a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), The Nation ta ruwaito.

Yayinda yake jawabi ga mabiya APC a taron nuna goyon baya ga gwamnan jihar, Hope Uzodinma, a Owerri, Chiji Collinsa ya ce yan majalisan shirye suke da baiwa gwamnan goyon baya domin nasara.

Ya jaddada cewa babu wanda ya biyasu kudi domin su sauya sheka.

Yace: "Zuwa daren jiya, yan majalisa 26 sun koma APC, kuma ina tabbatar muku a mako mai zuwa, dukkan 27 zasu zama APC. Ku jira zaman majalisa na gaba inda sukkansu zasu sanar da sauya shekansu."

"Shirye muke da goyawa gwamnan baya saboda ya shirya kawo sauyi jihar."

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

Tun daga ranar yan majalisan dokokin jihar suka fara sauka sheka zuwa jam'iyyar APC.

A jiya, Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sabon gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar shugaban kasa, AsoVilla, Abuja a ranar Juma'a, 31 ga Junairu, 2020.

Hope Uzodinma ya samu rakiyar shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Adams Oshiomole.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel