An tsinci gawar jami'in LASTMA rataye a allon sanarwa a Legas

An tsinci gawar jami'in LASTMA rataye a allon sanarwa a Legas

Hankulan mutane ya tashi a ranar Asabar yayin da suka gano gawar wani jami'in hukumar kula da dokar tuki da Legas (LASTMA), Tope Akinde tana lilo daga karfen allon sanarwa da ke kusa da Salvation Bus stop a unguwar Opebi da ke karamar hukumar Ikeja ta jihar Legas.

Mutane da dama sun taru a wurin da abin ya faru misalin karfe 9 na safe suna Allah wadai da dalilin da ya janyo mutuwar Akinde.

Wasu kuma a gefe guda suna kallon gawarwa na lilo daga karfen allon sanarwar da ke kusa da bishiyar mangwaro suna juyayin afkuwar lamarin.

Dandazon al'ummar da suka taru sun janyo cinkoson ababen hawa.

The Punch ta ruwaito cewa jami'an tsaro na unguwar sun ziyarci wurin da abin ya faru inda suka yi kokarin warware cinkoson ababen hawan.

Jami'in LASTMA ya rataye kansa a allon sanarwa a Legas, ya mutu
Jami'in LASTMA ya rataye kansa a allon sanarwa a Legas, ya mutu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

Wani ganau, Abiodun Fakemi ya ce ya hangi mutane sun taru suna kallon bishiya har ya yi tsamanin sun ga maciji ne amma da ya matsa kusa sai ya hangi gawar mutum tana lilo.

Ya ce: "Ina hanyar zuwa Salvation bus stop ne sai na ga dandazon mutane suna kallon bishiyar mangwaro. Ina tunanin katon maciji suka gani a bishiyar amma da na isa wurin sai na ga mutane suna daukan hoto da wayoyinsu. A wurin, akwai mutum yana lilo daga karfen allon sanarwa da harshensa a waje. Karfen yana kusa da bishiyar mangwaro ne kuma nan banagaren mutumin ya rataye kansa."

Da aka tuntubi mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Bala Elkana ya ce wata jami'an LASTMA ta sanar da rundunar afkuwar lamarin, ya kara da cewa yayan Akinde ya yi ikirarin cewa ya dade yana fama da tabin hankali.

Ya ce an dauke gawar an tafi da shi dakin ajiyar gawarwaki a asibitin IDH da ke Yaba a Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel