Yadda EFCC ta tsare ni a kurkukun karkashin kasa na tsawon kwanaki 30 - Shehu Sani

Yadda EFCC ta tsare ni a kurkukun karkashin kasa na tsawon kwanaki 30 - Shehu Sani

- Tsohon sanata daga jihar Kaduna, Shehu Sani ya bayyana yadda hukumar EFCC ta tsare shi a kurkukun karkashin kasa na tsawon kwanaki 30

- Shehu Sani ya ce an keta masa hakkinsa na dan adam yayin da ya ke tsare a hannun hukumar ta yaki da rashawa

- Sani ya zargi hukumar ta EFCC ta jefa shi cikin mawuyacin hali da tambayoyi masu tayar da hankali da kuma bincike gidansa da sunan neman kudin Dalla 24,000 ko 25,000 da ya karba

Tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana yadda jami'an hukumar yaki da rashawa ta EFCC suka tsare shi a wani kurkukun karkashin kasa na tsawon kwanaki 30 bisa umurnin shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

Shehu Sani, a wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a 1 ga watan Fabrairu, ya ce EFCC ta keta masa hakkinsa na dan adam kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yadda EFCC suka tsare ni a kurkukun karkashin kasa na tsawon kwanaki 30 - Shehu Sani
Yadda EFCC suka tsare ni a kurkukun karkashin kasa na tsawon kwanaki 30 - Shehu Sani
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Lafiya jari: Muhimman amfanin citta 4 a jikin dan Adam

Shehu Sani ya yi ikirarin cewa hukumar ta EFCC ta garkame shi a kurkukun karkashin kasa na tsawon kwanaki 30 bisa umurnin shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

Ya ce lokacin da ya ke tsare, hukumar yaki da rashawar ta masa tambayoyi masu tayar da hankali kuma sun bincike masa gida da ofis tare da tilasta masa ya bayyana kadarorinsa.

Tsohon dan majalisar ya ce jami'an hukumar sun rufe asusun ajiyan bankinsa, sun kwace wayoyinsa sun kuma nemi su tilasta masa yin amfani da na'urar gane masu karya.

Sani ya ce an tsare shi ne kan zargin cewa ya karbi dalla dubu 24 ko 25 wanda ya ce duk shaci-fadi ne, ya ce dukkan zargin da ake masa yayin da ya ke tsare karya ne.

Ya ce hukumar ta EFCC na iya masa sharri ama ba za ta taba hana shi kare kansa ba.

Sani ya yabawa kotu da ta bashi beli kuma ya yi alkawarin zai kiyaye dukkan ka'idojin belin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel