Hana 'yan Najeriya zuwa Amurka: Buhari ya kafa kwamiti na sulhu

Hana 'yan Najeriya zuwa Amurka: Buhari ya kafa kwamiti na sulhu

Fadar shugaban kasa ta yi martani a kan dokar hana wa wasu rukunin 'yan Najeriya shiga Amurka da gwamnatin kasar ta yi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti da za ta duba matakin da gwamnatin Amurkan ta dauka.

Kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin ministan harkokin cikin gida za ta yi nazarin sabbin ka'idojin da Amurka da gindaya da suka shafi batun tsaro da ake so gwamnatocin kasashen waje su rika bi.

Sanarwar da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter ya ce: "Kwamitin za ta yi aiki tare da gwamnatin Amurka, INTERPOL da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa an aiwatar da sabbin dokokin.

"Najeriya a shirye ta ke ta cigaba da karfafa kyakyawar alakar da ke tsakaninta da Amurka da sauran kawayen ta na kasashen waje musamman a kan harkokin tsaro na duniya."

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

A ranar Juma'a ne labarin ya wanzu a kafafen yadda labarai cewa Shugaba Donald Trump na Amurka ya saka dokar hana masu zuwa ci rani a Amurka bizar shiga kasar.

Dalilin da aka bayar shine Najeriya da wasu kasashe biyar da abin ya shafa ba su cika ka'idojin tsaro ko rashin bayar da hadin kai wurin magance tafiye-tafiye tsakanin kasashe ba bisa ka'ida ba.

Kafin sanarwar, akwai kishin-kishin cewa Najeriya na daga cikin kasashen da za a hana bizar shiga Amurka.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya nuna rashin jin dadinsa game da lamarin.

Ya ce 'yan Najeriya suna kaunar Amurka saboda haka bai dace a hukunta su saboda gazawar gwamnatin tarayya ba.

Ya bukaci mahukunta a Amurka su sake duba lamarin domin a samu maslaha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel