'Yan bindiga sun kashe matar likitan da suka sace a Kaduna, sun nemi a biya N20m a fanshi yaran ta

'Yan bindiga sun kashe matar likitan da suka sace a Kaduna, sun nemi a biya N20m a fanshi yaran ta

'Yan bindiga sun kashe matar wani likita mazaunin garin Kaduna, Philip Ataga bayan ta kwashe kwanaki bakwai a hannunsu.

Wadanda su kayi garkuwa da ita sun kashe ta ne bayan iyalan ta sun gaza biyansu Naira miliyan 150 da suka nema na fansar ta da 'ya'yan ta biyu da suka sace.

An sace su ne yayin da 'yan bindigan su kayi kutse a gidansu da ke Juji kusa da Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna a ranar 24 ga watan Janairu.

An kashe wani mai gadi a yayin harin da 'yan bindigan suka kai wanda hakan ya janyo zanga-zanga a ranar 25 ga watan Janairu. Matasa sun datse titin kachia inda suke neman a kawo karshen hare-haren da 'yan bindiga ke kai musu.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe matar likitan da suka sace a Kaduna, sun nemi a biya N20m a fanshi yaran ta
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe matar likitan da suka sace a Kaduna, sun nemi a biya N20m a fanshi yaran ta
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

Wata majiya da ke da kusanci da iyalan ya shaidawa The Cable a ranar Asabar cewa: "Yan bindigan sun kashe Mrs Ataga sannan suka jefar da gawarta a wani wuri kuma suka kira mijinta suka fada masa inda zai dauki gawar.

"An dauki gawar ta an kai shi dakin ajiye gawarwarki na asibitin Kwararru na Barau Dikko da ke Kaduna. Bayan kashe ta 'yan bindigan sun nemi a biya Naira miliyan 20 kafin su sako yaran."

Da aka tuntube shi domin samun karin bayani, Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna, Yakubu Sabo ya ce ba shi da masaniya cewar an kashe matar likitan.

Sabo ya ce: "A halin yanzu ba zan samu wannan rahoton ba amma zan tuntubi jami'an da ke binciken lamarin sannan in ba ku bayani."

Har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton kakakin 'yan sandan bai kira ya bayar da ba'asi kan afkuwar lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel