Ku yi hakuri, akwai sabon shirin da muke kokarin fito muku da shi kuma - Cewar Sadiya Umar Farouq ga ma'aikatan N-Power da za a kora

Ku yi hakuri, akwai sabon shirin da muke kokarin fito muku da shi kuma - Cewar Sadiya Umar Farouq ga ma'aikatan N-Power da za a kora

- Ministar walwala da ci gaban ‘yan kasa, Sadiya Umar Farouq ta ce masu aikin N-Power bai kamata su daga hankulansu ba

- Kamar yadda minsitar ta ce, gwamnatin tarayya ce ta daukesu kuma sun san na shekaru biyu ne amma rashin tsarin sallama yasa aka barsu har yanzu

- Ministar ta ce gwamnatin tarayya na da zabi masu tarin yawa wajen sallamarsu kuma za ta aminta da tsari daya don tabbatar da cewa basu koma gida sun zauna ba

Ministan walwala da ci gaban kasa, Sadiya Umar Farouq ta ce masu aikin N-Power bai kamata su daga hankulansu ba don kuwa gwamnati na shirye-shriyen yadda zasu kammala aiyukansu.

Faruq ta sanar da hakan ne a Abuja yayin da ta kai ziyara ga hedkwatar Media Trust Limited, mawallafan jaridar Daily Trust.

Ku yi hakuri, akwai sabon shirin da muke kokarin fito muku da shi kuma - Cewar Sadiya Umar Farouq ga ma'aikatan N-Power da za a kora
Ku yi hakuri, akwai sabon shirin da muke kokarin fito muku da shi kuma - Cewar Sadiya Umar Farouq ga ma'aikatan N-Power da za a kora
Asali: UGC

“Ban san abinda suke tsoro ba amma na san gwamnati ce ke da shirin N-Power din kuma ta tabbatar da cewa na shekaru biyu ta daukesu. Wadanda suka fara a 2016 ya kamata su kare ne a 2018 amma saboda ba a tsara tafiyarsu ba aka bar su har yanzu. Dama tun farko sun san ba dindindin aka daukesu ba. A matsayin ma’aikatarmu, muna duban yadda za a yi su kammala lafiya.” Cewar ministan.

KU KARANTA: Matana 4 kuma ina alfahari da al'adarmu, ko yanzu aka ce na kara zan karo wasu - Tsohon mai taimakawa shugaban kasa

Ta kara da cewa, “Bai kamata mu barsu su tafi haka nan ba. Muna da zabuka kuma zamu yi amfani dasu wajen sallamarsu ba tare da sun koma gidan jiya ba. Yanzu shekarar ta fara kuma muna fatan kafin karshen shekarar zamu fito da tsarin sallamarsu,”

Ta ce wannan shirin ciyar da yara ‘yan makaranta ya samu nasarori masu tarin yawa a kusan dukkan jihohin da suka fara. Ta ce ma’aikatar na kokarin ganin ta inganta rayuwar ‘yan gudun hijira da ke yankin Arewa maso gabas din kasar nan, amma ba za ta mayar dasu yankunansu ba har sai ta tabbatar da babu sauran matsala a yankunan.

Ta ce ma’aikatar ta na fatan samun dangantaka mai amfani tsakaninta da Media Trust don tabbatar da shawo kan matsalolin ‘yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel