Hukumar EFCC ta kama tsohon dan takarar gwamna da ya yi karar ta a kotu

Hukumar EFCC ta kama tsohon dan takarar gwamna da ya yi karar ta a kotu

Hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama dan takarar gwamna na jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) a zaben shekarar 2019 a jihar Anambra, Chief Ifeanyichukwu Okonkwo.

Hukumar yaki da rashawar ta kama Okonkwo ne bayan ya yi karar ta a kotu inda ya ke neman a biya shi diyyar Naira miliyan 65.

Saturday Punch ta ruwaito cewa hukumar ta EFCC a baya ta tsare mai rajin kare hakkin bil adaman na tsawon kwanaki biyu sannan ta saki shi beli.

Sai dai bayan watanni 18 da bayar da shi belin, hukumar ta EFCC ta gaza gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin da ta ke masa na samun wasu kudade masu yawa ta haramtattun hanyoyi.

Okonkwo ya yi karar hukumar kan tsare shi ba bisa ka'ida ba, yi masa barazana da rufe asusun ajiyarsa na banki tun watan Mayun 2019 ba tare da samun izini daga kotu ba.

Hukumar EFCC ta kama tsohon dan takarar gwamna da ya yi karar ta a kotu
Hukumar EFCC ta kama tsohon dan takarar gwamna da ya yi karar ta a kotu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani mutum ya mutu yayin da ya ke zina da wata budurwa a otel

Hukumar ta EFCC ta sake kama Okonkwo nan take bayan kotun ta daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar Litinin.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa a baya Okonkwo ya taba yin karar shugaban riko na hukumar EFCC, Ibrahim Magu inda ya koka kan yadda hukumar na yankin Kudu maso gabas ke gudanar da ayyukan ta.

A wani rahoton mun kawo muku cewa hukumar ta EFCC ta haramtawa mutane masu aure shiga sahun masu neman aikin hukumar.

Hukumar ta bada wannan sanarwar ne a cikin ka'idojin da mai neman aiki a hukumar zai cike kafin a dube shi.

Wannan hukuncin kuwa ya jawo musu cece-kuce daga Nigeria Employers Consultative Association, NECA, kungiyar da ke da dangantaka da kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC.

Babban daraktan NECA, Timothy Olawale, ya sanar da jaridar The Punch cewa wannan dokar ta EFCC ta sha banban da dokokin kungiyar kwadago ta duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel