Coronavirus: 'Yan Najeriya da ke China ba su son dawowa gida - Lai Mohammed

Coronavirus: 'Yan Najeriya da ke China ba su son dawowa gida - Lai Mohammed

Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa 'yan Najeriya mazauna birnin Wuhan a kasar China da aka samun bullar Coronavirus sun bayyana cewa ba su da niyyar dawowa gida Najeriya.

Da ya ke jawabi yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma'a, 31 ga watan Janairu, Lai Mohammed ya ce tuni sun tuntubi 'yan Najeriya 16 da ke zaune a birnin Wuhan.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ba za ta iya hana 'yan Najeriya tafiya kasar China ba duk da bullar anobar cutar da Coronavirus.

"Mun san hana mutane yin tafiya abu ne mai wahala.

Coronavirus: 'Yan Najeriya da ke China ba su son dawowa gida - Lai Mohammed
Coronavirus: 'Yan Najeriya da ke China ba su son dawowa gida - Lai Mohammed
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

"Wani abu kuma shine wannan ba dalili bane da zai sa a fara tsangwar mutanen da suka fito daga kasar.

"Ko da akwai 'yan Najeriya da ke zaune a can, ba za mu iya tilasta musu dawowa gida ba idan har ba su nuna cewa suna son su dawo ba.

"Na san akwai 'yan Najeriya a Wuhan; ofishin jakadancin mu na China ya tabbatar da cewa akwai kimanin 'yan Najeriya 16 a birnin ta Wuhan kuma mun tuntube su.

"Muna bukatar wayar da kan mutane sosai. Muna son mutane su rika fadin gaskiya a duk lokacin da suke cika fom."

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Najeriya ta fitar da gargadi ga matafiya, inda ta shawarci su dena zuwa kasar China saboda bullar cuta mai kama da murar kaji da ke bazuwa a kasar ta China.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel