Mai wa'azin addinin Kirista ya nemi gafara kan kalaman batanci da ya yi game da Musulunci

Mai wa'azin addinin Kirista ya nemi gafara kan kalaman batanci da ya yi game da Musulunci

Wani malamin addinin Kirista karkashin darikar Katolika a Minnesota da ke Amurka ya bai wa musulmai hakuri a kan kiran Musulunci da ya yi da “babban kalubalen da duniya ke fuskanta”.

Rabaren Nick VanDenBrooke ya bada hakurin ne a ranar Laraba a wani rubutu da ya wallafa a shafin Archdiocese of St. Paul da Minnesota a karkashin tsokacin shi na wallafar da yayi a ranar 5 ga watan Janairu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, “Shawarata a kan mutane masu shige da fice na dauke da kalaman da suka bata wa Musulmai rai. Ina basu hakuri don na gano cewa tsokaci na basu yi dai-dai da koyarwar cocin Katolika ba a kan Musulunci."

Wannan rokon yafiyar ko gafarar ya biyo bayan bukatar da cibiyar kula da Musulmai ‘yan Amurka ta mika gaban reshen Minnesota din a kan su janye kalaman kiyayya da suka hada da sukar addinin Musulunci.

Malamin addinin Kirista ya nemi gafara kan kalaman batanci da yayi ga Musulunci
Malamin addinin Kirista ya nemi gafara kan kalaman batanci da yayi ga Musulunci
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Maciji ya kashe wani mai wasa da macizai yayin da ya ke nuna bajintarsa (Bidiyo)

Yin shiru a kan wannan zancen zai nuna cewa mun rike cocin ne,” kungiyar ta sanar a wata takarda.

A yayin bayyana Musulunci a matsayin babban kalubale a duniya ga Amurka da kuma Kiristoci, VanDenBrooke ya bukaci Amurka da ta dena tunanin karbar kowanne mai shiga kasar dai-dai, cewar kungiyar.

“Ina tunanin akwai bukatar a dubi addini da kuma masu shiga kasa ko masu gudun hijira a duk fadin duniya,” VanDenBrooke ya sanar da masu bauta kamar yadda CAIR ta ruwaito.

“Gaskiya bai kamata ana barin Musulmai masu tarin yawa na samun mafaka ko kuma shigowa kasar mu ba,” Jaridar New York ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel