Yadda wani mutum yake tilasta ma matarsa kwanciya da shi yayin da take haila

Yadda wani mutum yake tilasta ma matarsa kwanciya da shi yayin da take haila

Zo mu zauna, zo mu saba, kamar yadda masu iya magana suke fadi, hakan kuma ya fi tabbata musamman a tsakanin ma’aurata, walau ko su suka hada kansu a auren soyayya ko kuma auren dole aka yi musu.

A wannan karo zama bai yi dadi ba tsakanin wasu ma’aurata biyu, wanda ta kai ga har uwargida ta garzaya gaban Alkali kotu tana neman kotun ta kawo karshen aurenta da mijinta, kuma uban yaranta.

KU KARANTA: Kunar bakin wake ya dawo a Maiduguri: Karamar yarinya ta kashe mutane 3 a Islamiyya

Wannan mata ta gurfana ne a gaban babbar kotun lardi dake garin Jiwa, na babban birnin tarayya Abuja, inda ta yi karar mijinta, wanda tace yana tilasta mata yin sallah da kuma kwanciya da ita a duk lokacin da take jinin al’ada.

Jaridar Aminiya ta ruwaito a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu aka yi wannan zama na kotu, inda mamaki ya cika mahalarta kotun, saboda dukkanin abubuwan da matar take zargin mijin da aikatawa sun saba ma koyar addinin musulunci karara.

Bayan sauraron bangaren matar, Alkalin kotun mai sharia Muhammad B Marafa ya bayyana ma wanda ake kara cewa dukkanin bukatunsa biyu ga matar sun saba da karantarwar Qur’anin Allah da kuma koyarwar Annabi Muhammad (S.A.W) dake cikin hadisai.

A wani labarin kuma, rahotanni sun tabbatar da cewa matasa masu yi ma kasa hidima sun fara samun sabon alawus na naira dubu talatin da uku (N33,000) kamar yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauki alkawari.

A cikin wannan makon ne shugaban hukumar NYSC, Shuaibu Ibrahim ya sanar da karin kudin alawus din, inda yace yana sa ran nan bada jimawa ba gwamnati za ta fara biyan kudin bayan samun amincewa daga shugaban kasa.

Sai ga shi kwatsam a ranar Alhamis yan bautan kasa sun fara samun sakon shigar kudi na bankuna dake tabbatar musu da sabon albashin, yan bautan kasa masu amfani da bankin Zenith ne suka fara samun kudin, yayin da sauran bankunan suka fara biya a ranar Juma’a, 31 ga watan Janairu.

Kafin wannan kari, yan bautan kasa suna amsan N19,000 ne a matsayin alawus dinsu na wata wata, shi ma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya yi musu wannan karin a shekarar daya kara karancin albashi zuwa N19,000.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel