Ma'aurata 53 suka kashe kawunansu tsakanin Nuwamban 2017 da Maryam Sanda ta kashe mijinta kawo yanzu

Ma'aurata 53 suka kashe kawunansu tsakanin Nuwamban 2017 da Maryam Sanda ta kashe mijinta kawo yanzu

- Kashe-kashe tsakanin ma'aurata ya zama ruwan dare a dukkan sassan Najeriya cikin shekaru biya da suka gabata

- Wanda ya fi shahara shine wanda ya faru a birnin tarayya Abuja inda Maryam Sanda ta hallaka mijinta, Bilyaminu Halliru, ga sabani da suka samu

- Bayan watanni 26 ana shari'ar, Alkalin kotu, Yusuf Halilu, ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya

Akalla ma'aurata 53 suka kashe kawunansu a Najeriya tsakanin 19 ga Nuwamban 2017, da Maryam Sanda ta kashe mijinta kawo yanzu. Binciken Daily Trust ya bayyana.

Watanni 26 bayan kisan mijinta, kotu ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Bayan haka, wani mutum mai suna Bamidele Olanrewaju, a jihar Ogun ya hallaka matarsa, Adenike, a ranar Lahadi, 19 ga Junairu, 2020 a gidansu dake kauyen Bisodun, karamar hukumar Obafemi-Owode, jihar Ogun, kakakin hukumar yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya tabbatar.

Hakazalika, wani mutum dan shekara 60 a Ile-Ife, jihar Osun, Rafiu Irawo, ya kashe matarsa, Funke, kan zarginta da zina da wani mutumi sannan ya kashe kansa a ranar Juma'a, 20 ga watan Satumba, 2019.

Gabanin haka, an tuhumci wata mata mai suna Akorede Balogun, da laifin kashe mijinta, Rasaki Balogun, a cikin gidansu dake No. 16, Taiwo Oke Street, Victory Estate, Ejigbo tare da wata karuwa, Muyibat Alabi, ranar 10 ga Yuli, 2019 a jihar Legas.

Ma'aurata 53 suka kashe kawunansu tsakanin Nuwamban 2017 da Maryam Sanda ta kashe mijinta kawo yanzu
Maryam Sanda ta kashe mijinta kawo yanzu
Asali: UGC

DUBA NAN: Karin kudin Hara: Yan Najeriya zasu fuskancin karin kudin kiran waya da Data - Kamfanonin Sadarwa

A jihar Ogun a Disamban, 2019, wani mutum mai suna Mutiu Sonola, ya shiga hannun hukumar yan sandan jihar kan laifin dukan matarsa, Zainab Shotayo, har lahira.

Hakazalika ranar 27 ga Junairu 2020 misalin karfe 4 na Asuba, wata amarya ta burmawa mijin, Shamsuddeen Salisu, wuka har lahira a karamar hukumar Malumfashin jihar Katsina.

A karshe, binciken ya nuna cewa mata 36 sun rasa rayukansu ta hannun mazajensu yayinda maza 17 suka hallaka ta hannun iyalansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel