Na rabu da saurayina, saboda idan mutum yayi yaudara a garinsu mutuwa yake take a wajen

Na rabu da saurayina, saboda idan mutum yayi yaudara a garinsu mutuwa yake take a wajen

- Soyayya mai inganci na tafiya ne tare da rikon amana ta yadda komai rintsi ko wuya zaka kasance da masoyin naka

- Wata budurwa ta wallafa yadda ta firgice tare da barin saurayinta bayan ya sanar da ita dokar kauyensu matukar mace ta ci amanar saurayi ko miji

- Matukar budurwa ta ci amanar saurayi, tana haukacewa ne. Ita kuwa matar aure mutuwa take yi idan ta ci amanar mijinta

Soyayya mai inganci tare da rikon amana na da dadi. Iya rike amanar masoyi kuwa na da wuya a tsakanin mata da mazan zamanin nan. Sau da yawa zaka ga mace da samari sama da biyar, haka suma mazan ba a barinsu a baya wajen tara 'yan mata.

Wata budurwa 'yar Najeriya ta wallafa bayanin firgici da tsoron da ta shiga wanda yasa ta bar soyayya da saurayinta.

Na rabu da saurayina, saboda idan mutum yayi yaudara a garinsu mutuwa yake take a wajen
Na rabu da saurayina, saboda idan mutum yayi yaudara a garinsu mutuwa yake take a wajen
Asali: Facebook

Budurwar ta bayyana cewa ta bar saurayinta ne gudun haukacewa. Saurayin nata ya sanar da ita cewa matukar aka ci amanar shi toh mutuwa ake yi. Wannan kuwa al'adar kauyensu ce don mace haukacewa take idan ta ci amanarsu.

Kamar yadda budurwar ta bayyana, matukar matar mutum kuwa ta ci amanar shi a al'adar kauyen, a take za ta mutu. Amma kuma matukar mijin ne ya ci amanar, babu abinda ke faruwa.

KU KARANTA: 'Yan Karota zasu fara kamen baburan adaidaita a jihar Kano

Ga abinda ta wallafa: "A al'adar kauyen sabon saurayina, matukar mace ta ci amanar saurayinta, toh haukacewa take yi. Idan kuwa matar mutum ce ta ci amanar, mutuwa take yi a take. Shi kuwa namiji ko ya ci amana, babu abinda ke faruwa da shi.

"Na ga ba zan iya wannan yarjejeniyar bane, shiyasa na tsere na bar shi. Bana bukatar yin hauka ko kuma in mutu lokaci na bai yi ba." Cewar budurwar.

Jaridar Nigerian Bulletin ce ta wallafa tare da hoton budurwar kamar yadda ta labarta a shafinta na tuwita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel