Da duminsa: Ana artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Damasak yanzu haka

Da duminsa: Ana artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Damasak yanzu haka

Labarin da muke samu daga majiya mai siqa a Borno na nuna cewa ana musayan wyta tsakanin dakarun Sojojin Najeriya da yan ta'addan Boko Haram a gairn Damasak ta jihar.

Kana SaharaReporters ta bayyana cewa ana artabu a yanzu haka.

Majiya ya bayyana cewa: "Ku yiwa Sojojinmu dake Damasak addu'a, yan Boko Haram sun kai musu hari."

"Ko a jiya an dakile irin wannan harin kuma gashi yau sun sake dawowa da yamman nan. Muna addu'a Sojinmu su samu nasarar wannan."

Da duminsa: Ana artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Damasak yanzu haka
Da duminsa: Ana artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Damasak yanzu haka
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa wasu mayakan Boko Haram sun kai mummunan hari a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda suka tare wata mota dake dauke da fasinjoji, suka yi ma guda uku daga cikinsu yankan rago.

Daily Trust ta ruwaito wata majiya daga rundunar tsaro ce ta tabbatar mata da aukuwar lamarin, inda yace yan ta’addan sun tare hanyar ne da yammacin ranar Talata, 28 ga watan Janairu a daidai garin Auno na karamar hukumar Konduga.

Majiyar ta bayyana cewa motar fasinjojin ta mutu ne a kan hanyar sakamakon wata matsala da ta samu, wanda hakan ya tilasta ma fasinjojin motar fitowa domin gyaran motar, a daidai wannan lokaci ne Boko Haram suka bayyana.

Isarsu inda fasinjojin suke ke da wuya, sai yan ta’addan suka kwantar da guda uku daga cikinsu, suka musu yankan rago da adda, yayin da na hudunsu yake cikin mawuyacin hali a yanzu haka sakamakon raunin daya samu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel