Maciji ya kashe wani mai wasa da macizai yayin da ya ke nuna bajintarsa (Bidiyo)

Maciji ya kashe wani mai wasa da macizai yayin da ya ke nuna bajintarsa (Bidiyo)

Wani mai wasa da macizai ya mutu bayan wani macijin da yake wasa da shi ya cije shi yayin da yake nishantar da wasu mutane a wani kauye.

Mai wasa da macijin, Norjani ya kama katon macijin ne a makon da ya gabata a yammacin Kalimantan a kasar Indonesia. Ya rufe shi cikin akwatin katako don yi masa maganin gargajiya sannan ya fito da shi ranar Asabar 25 ga watan Janairun 2020 don ya nuna wa makwabta.

A cikin bidiyon da ke yawo a dandalin sada zumunta, an gano Norjani yana wasa da macijin. Yana cikin hakan kwatsam macijin ya fusata ya kai masa cizo a hannu.

Da mutanen kauyen suka matso kusa domin su taimaka masa sai ya yi nuni da hannunsa cewa su kyalle shi kuma ya cigaba da wasar da ya ke yi da macijin.

Awanni biyu bayan kammala wasa da macijin, ya fara jin ba dai-dai ba a jikinsu inda aka garzaya da shi asibiti likitoci suka bashi maganin maciji amma sai dai dafin macijin ya riga ya bi jikinsa, a yammacin ranar aka sanar da cewa ya mutu.

Mazauna kauyen sun shiga dimuwa hakan yasa suka kashe macijin ta hanyar datse kansa, da nufin daukan fansa kan aljannun da ke jikin macijin.

Shugaban 'yan sanda Dede Hasanudin ya ce lamarin ya faru a kauyen Pak Utan inda Norjani ya yi suna wurin yin abubuwan mamaki da dabobi.

DUBA WANNAN: Wani da su kayi karatu tare da Maryam Sanda ya fadi irin halayenta da ya sani

Dan sandan ya ce: "Eh, da gaske ne Norjani ko kuma Nek Tadong kamar yadda aka kiran sa wasu lokuta ya mutu sakamakon cizonsa da maciji ya yi.

"Misalin karfe 6 na yamma aka kai shi asibiti a Menjalin aka yi masa magani amma ya mutu saboda ya yi jinkirin zuwa asibitin.

"Anyi jana'izarsa bayan kwana guda kuma 'yan uwansa sun kashe macijin.

"Mazauna kauyen sun san shi sosai kuma yana kiwon dabobi daban-daban. Ya na bawa muatne magungunan gargajiya har ana yi masa lakabi da mai maganin kauyen."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel