Jonathan ya yi magana kan kallubalen tsaro a Najeriya

Jonathan ya yi magana kan kallubalen tsaro a Najeriya

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce mutane da dama suna fadawa cikin fitintinu sakamakon yaduwar rashin tsaro a kasar nan.

Jonathan ya bayyana hakan na yayin da kungiyar daliban Najeriya na kasa (NANS) ta kai masa ziyarar goyon baya a kan harin da aka kai gidansa da ke Bayelsa a watan December.

A cewar mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, tsohon shugaban kasar ya fadawa tawagar cewa yana matukar damuwa kan makomar talakawan Najeriya idan har duk da matsayinsa shima bai tsira ba.

Ya kara da cewa rasuwar wani soja sakamakon harin ya matukar bakanta masa rai inda ya ce, "ba domin gadi na ya ke yi ba da mutumin bai mutu ba."

Jonathan ya yi magana kan kallubalen tsaro a Najeriya
Jonathan ya yi magana kan kallubalen tsaro a Najeriya
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Wani da su kayi karatu tare da Maryam Sanda ya fadi irin halayenta da ya sani

"Duk lokacin da na tuna cewa mutane za su iya yi wa tsohon shugaban kasa da ke da masu gadinsa haka, tunani na ya kan koma kan sauran 'yan Najeriya da ba su da irin tsaron da na ke da shi.

"Na damu saboda 'yan Najeriya da dama suna fuskantar kallubale na 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauransu. Na yi imanin cewa kasar za ta magance wannan matsalolin da ke fama da shi na rashin tsaro."

Jawabin na Jonathan na zuwa ne yayin da ake ta maganganu kan kallubalen rashin tsaro a kasar.

A ranar Laraba ne majalisar wakilai da ta dattijai suka bukaci shugabannin hukumomin tsaro su yi murabus daga ayyukansu idan ba za su iya magance kallubalen tsaro da ke fama da shi a kasar ba.

Tsohon shugaban kasar yana gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock Villa a ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel