Gwamna Bagudu ya nada masu bashi shawara 140

Gwamna Bagudu ya nada masu bashi shawara 140

Gwamnan Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya amince da nadin masu bayar da shawara na musamman (SAs) 40 da kuma manyan masu bayar da shawara na musamman (SSAs) guda 100.

Sakataren gwamnatin jihar, Babale Yauri ne ya bayar da sanarwar a yayin taron manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar a ranar Alhamis.

Ya ce, "Bayan taron majalisar zartarwar na jihar karo na farko da aka gudanar a yau, dukkan 'yan majalisar gwamnatin jihar sun amince za suyi aiki tare domin tallafawa Bagudu wurin cimma kudirorinsa na kawo cigaba da jihar."

Gwamna Bagudu ya nada masu bashi shawara 140
Gwamna Bagudu ya nada masu bashi shawara 140
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda matar aure da kwartonta suka fatattaki mai gida daga gidansa bayan ya kama su suna lalata

Mista Yauri ya ce Gwamna Bagudu ya kuma rarrabawa sabbin kwamishinoni da aka nada ma'aikatun da za suyi aiki inda ya kara da cewa ayyukansu zai fara nan take.

Wasu daga cikin kwamishinonin sun hada da:

1. Ramatu Gulma - Ma'aikatan Shari'a

2. Ibrahim Augie - Ma'aikatan Kudi

3. Alhaji Kangiwa - Ma'aikatan albarkatun ruwa

4. Kaliel Gidado - Ma'aikatan matasa da wasanni

5. Rakiya Ayuba - Ma'aikatan Cinikayya da masana'atu da

6. Mamuda Warra - Ma'aikatan watsa labarai da al'adu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel