Buhari kadai zai iya kawar da Boko Haram - Fadar shugaban kasa

Buhari kadai zai iya kawar da Boko Haram - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ne mutum daya tilo da zai iya kawo karshen yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya da suka addabi al'umma.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba, 29 ga Junairu, 2020.

Garba Shehu yace: "Shugaba Buhari zai kawo karshen wadannan yan ta'addan. Shi kadai zai iya."

Garba Shehu ya bayyana hakan ne a martani da ya yi ga Sanata Abaribe da ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus daga kujerarsa a matsayin shugaban kasa saboda ikirarin da ya yi na cewa shugaban kasar ya gaza magance kallubalen tsaro da ke adabar kasar.

Hakan ya biyo bayan kiran da yan majalisar wakilai da dattawa sukayi a jiya na Buhari ya sallami hafsoshin tsaro.

Mambobin majalisar sun yi kira ga shugabannin tsaro da su yi murabus daga kujerunsu ko kuma a fitittikesu.

A martanin da ya yi da shafinsa na Twitter @GarShehu ya ce kiran da Abaribe ya yi na cewa Buhari ya yi murabus 'sakarci ne'.

A yau Alhamis, Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da masu bashi shawara kan tsaro da hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban kasa, AsoVilla, Abuja.

Daga cikin wadanda ke hallare sune sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma'aikatan Buhari, Abba Kyari; ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi; ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; da mai bada shawarar tsaro, Babagana Munguno da sauransu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel