Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama tsohon ministan man fetur, Dan Etete

Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama tsohon ministan man fetur, Dan Etete

- Justis Idris Kutigi ya ya ba Sufeto Janar na yan sanda, Adamu Muhammad umurnin kama tsohon ministan man fetur, Dan Etete

- Ana zargin tsohon ministan da kasancewa da hannu a cikin badakalar man Malabu

- Kutigi ya kuma yi umurnin gabatar da tsohon ministan a gaban kotu bayan kama shi

Justis Idris Kutigi ya yi umurnin kama tsohon ministan man fetur, Dan Etete kan kasancewarsa da hannu a badakalar man Malabu.

Mai kara, Bala Sanga, a wani bukata da ya gabatar ya sanar da kotu cewa kama Mista Etete na da muhimmanci sosai wajen gano gaskiya lamari game da badakalar man Malabu.

Justis Idris Kutigi, yayinda ya ke amsa bukatar, ya ba Sufeto Janar na yan sanda, Adamu Muhammad umurnin kama tsohon ministan sannan su gabatar dashi a gaban kotu.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a bayan cewa Wata babbar kotun birnin tarayya dake zamanta a Gwagwalada ta baiwa tsohon Antoni Janar na zamanin Jonathan, Mohammed Adoke, belin N50m.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da Adoke ne tare da shugaban kamfanin man Malabu oil and Gas Limited, Aliyu Abubakar, da Rasky Gbinigie, na kamfanin Agip, kan laifuka 42 na rub da ciki da babakere.

KU KARANTA KUMA: Hajji: Zan zabtare kudin mahajatta – Zababben Shugaban NAHCON ya yi alkawari

EFCC ta yi zargin cewa Adoke ya amshi cin hancin N300 million daga hannun Aliyu kan rijiyar man OPL 245. Adoke ya musanta dukkan zarge-zargen 42 da ake masa gaban kotu.

A wani labarin kuma mun ji cewa EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta gurfanar da Mista Azubuike Ishiekwene a gaban Alkali a Ranar Laraba.

Rahotanni sun ce ana zargin Azubuike Ishiekwene da laifin da su ka shafi buga takardun bogi da nufin damfarar kudin da sun kai Naira miliyan 350.

EFCC ta shigar da karar tsohon Darektan na gidan jaridar Punch gaban Alkalin wani kotu na laifuffuka na musamman da ke Garin Ikeja a jihar Legas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel