Ado Doguwa ya gabatar da matansa 4 gaban yan majalisa, ya ce yara 27 suka haifa masa

Ado Doguwa ya gabatar da matansa 4 gaban yan majalisa, ya ce yara 27 suka haifa masa

- Dan majalisan wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana yawan 'yayan da ya haifa

- Dan majalisan ya gabatar da matansa hudu gaban yan majalisa yayinda aka rantsar da isa

- Ado Doguwa ya bayyanawa takwarorinsa cewa yana sa ran cigaba da hayayyafa

Dan majalisan wakilan tarayya mai wakiltan mazabar Tudun Wada/Doguwa, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa 'yaya 27 matansa hudu suka haifa masa kuma zasu cigaba da hayayyafa.

Yayinda ake zaman majalisa ranar Laraba, Doguwa ya gabatar da matansa hudu gaban yan majalisa.

Yayinda ake rantsar da shi matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar, ya bayyana cewa ya kawo matansu hudu domin yan majalisa su gansu.

"Kakin majalisa, ina mai farin cikin fada muku cewa mata na hudu na tare da ni a nan yau," Doguwa ya laburta , kafin umurtan matan su mike tsaye gaban yan majalisa.

"Ya mai girma kakakin majalisa, wadannan mata nawa hudu da kuke gani sun haifa masa 'yaya 27, kuma muna cigaba."

Ado Doguwa ya gabatar da matansa 4 gaban yan majalisa, ya ce yara 27 suka haifa masa
Ado Doguwa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kotu ta baiwa tsohon Antoni Janar, Mohammed Adoke, belin N50m

Hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC ta alanta Alhassan Ado Doguwa, matsayin zakaran zaben mai-mai na mai wakilatan mazabar Tudun Wada/Doguwa a majalisar wakilan tarayya.

Baturen zaben, Farfesa Mansur Bindawa, ya bayyana cewa Ado Doguwa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya samu kuri'u 66,667 yayinda abokin hamayyarsa Yusha’u Salisu na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ya samu kuri'u 6,323 .

Za ku tuna cewa a ranar 4 ga Nuwamba, 2019, kotun daukaka kara dake zauna a Kaduna ta fitittiki Ado Doguwa wanda yake shugaban masu rinjaye a majalisar, tun ta bada umurnin sabon lale.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel