Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro

Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da masu bashi shawara kan tsaro da hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban kasa, AsoVilla, Abuja.

Daga cikin wadanda ke hallare sune sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma'aikatan Buhari, Abba Kyari; ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi; ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; da mai bada shawarar tsaro, Babagana Munguno.

Hafsoshin tsaron da cikin ganawar sune shugaban hukumar tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; babban hafsan sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai; babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; babban hafsan sojin sama, AM Sadique Baba.

Sauran sune sifeto janar na yan sanda, IGP Mohammed Adamu; shugaban hukumar leken asiri NIA, Ahmed Rufa'i Abubakar; diraktan DSS, Yusuf Magaji Bichi.

An kaddamar da zaman ne misalin karfe 10 na safe kuma majiyoyi sun bayyana cewa ana tattaunawa ne kan matsalolin tsaron da suka ki ci, suka ki cinyewa.

KU KARANTA: Kotu ta baiwa tsohon Antoni Janar, Mohammed Adoke, belin N50m

Wannan ya biyo bayan kiran da yan majalisar wakilai da dattawa sukayi a jiya na Buhari ya sallami hafsoshin tsaro.

Mambobin majalisar sun yi kira ga shugabannin tsaro da su yi murabus daga kujerunsu ko kuma a fitittikesu.

Wannan shine matsayar yan majalisar bayan sun yi muhawara kan lamarin tsaron kasar a zamansu na ranar Laraba, 28 ga watan Janairu a Abuja.

Wani dan majalisa, Abubakar Fulata, ya sanar da takwarorinsa a zauren majalisar cewa shugabannin tsaron sun yasar da amfaninsu.

A cewarsa, kasar za ta kasance cikin hatsari idan aka bar wadannan mutane suna cigaba da maimaita abu guda tare da sa ran samun banbancin sakamako wajen yaki da matsalolin tsaron da ke addabar kasar.

Hakazalika, Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus kan gazawar gwamnatinsa wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng