Kano: Dan takarar PDP da ya kayar da Abdulmumi Kofa yana shirin koma wa APC

Kano: Dan takarar PDP da ya kayar da Abdulmumi Kofa yana shirin koma wa APC

Ali Datti-Yako, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata na ranar Asabar a mazabar Kiru/Bebeji na tarayya, an gano cewa yana shirin komawa jam'iyyar APC.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Yako ya kayar da tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar, Abdulmumin Jibrin, da tazarar kuri'u 35,094.

A yayin da ake ta kokarin yin zaben maye gurbin, majiyoyi masu yawa sun ce manyan jam'iyyar APC na jihar Kano sun yi yarjejeniya da Yako a kan zai koma jam'iyyar bayan yayi nasara a zaben.

Kwanaki biyu kacal bayan sanar da nasarar dan majalisar, an ga hotonsa rike da shahadar komawa majalisa tare da shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas.

Kano: Dan takarar PDP da ya kayar da Abdulmumi Kofa yana shirin koma wa APC
Kano: Dan takarar PDP da ya kayar da Abdulmumi Kofa yana shirin koma wa APC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Himba: Kabilar da mata basa wanka amma da mace ake karrama bako

Wani hoton Yako kuwa ya fito ne inda yake yin hannu da Gwamna Abdullahi Ganduje, nufin tsananin alaka mai karfi da jam'iyyar mai mulki.

Duk da Yako bai fito ya bayyana cewa ya bar PDP ba, majiyar da ta bukaci a sirranta ta, ta sanar da jaridar Daily Nigerian cewa shugabannin jam'iyyar APC na shirya gagarumar walima don sabon dan majalisar.

Wasu majiyoyi kuwa sun ce Yako, wanda makusanci ne ga Hamza Maifata na jam'iyyar PDP, yana yaudarar shugabannin jam'iyyar APC ne kawai don ba shi da niyyar barin jam'iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel