Carabao: Man Utd sun tadawa Man City hankali duk da jan kati
A jiya ne aka buga wasan daf da karshe a gasar cin kofin Carabao tsakin kungiyar kwallon kafa na Manchester United da kuma ta Manchester City.
Wannan wasa ta tashi 1-0 ne da nasara a kan Manchester United. Sai dai duk da wannan nasara, an yi waje da kungiyar daga gasar karamin kofin.
Kungiyar Manchester United ta yi waje ne bisa la’akari da jimillar kwallon da aka zuba, City ta samu nasarar fitowa wasan karshe ne da ci 3-2.
Nemanja Matic shi ne ya zurawa Manchester United kwallo tun a zangon farko a daidai minti na 35. Wannan kwallo ta makale har aka tashi wasan.
Bayan mintuna 40 da jefa kwallo a raga, Alkalin wasa ya sallami ‘Dan wasan tsakiya N. Matic bayan ya sake aikata laifin gargadi a karo na biyu.
KU KARANTA: Wasu Magoya bayan Man Utd sun fara gajiya da Ed Woordward
Manchester United ta buga wasa na kusan rabin sa’a da ‘Yan wasa 10 bayan ta samu jan kati. Duk da haka wannan bai hana ta yi wa City barazana ba.
A wasan farko da aka buga, Manchester City sun doke Abokan hamayyarsu kuma manyan makwabtansu watau Manchester United da ci 3-1.
Bayan wannan wasa, Yaran Pep Guardiola za su gwabza da Aston Villa a wasan karshe na neman kofin a babban filin kwallon Ingila da ke Wembley.
Manchester City ta ci kwallo a wasan amma Alkalai su ka soke saboda satar hanya. A karshen wasan Guardiola ya ce sai sun kara yi da gaske a gaba.
Sergio Aguero, Riyad Mahrez, Raheem Sterling da Kevin de Bruyne duk sun buga wasan. Wannan ne karon farko da aka doke City a wasan kofi tun 2017.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng