Mayakan Boko Haram sun tare hanyar Damuturu, sun fille kawunan mutane 3

Mayakan Boko Haram sun tare hanyar Damuturu, sun fille kawunan mutane 3

Wasu mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta kai mummunan hari a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda suka tare wata mota dake dauke da fasinjoji, suka yi ma guda uku daga cikinsu yankan rago.

Daily Trust ta ruwaito wata majiya daga rundunar tsaro ce ta tabbatar mata da aukuwar lamarin, inda yace yan ta’addan sun tare hanyar ne da yammacin ranar Talata, 28 ga watan Janairu a daidai garin Auno na karamar hukumar Konduga.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya bayyana manyan kalubalen da ake fuskanta a yaki da ta’addanci

Majiyar ta bayyana cewa motar fasinjojin ta mutu ne a kan hanyar sakamakon wata matsala da ta samu, wanda hakan ya tilasta ma fasinjojin motar fitowa domin gyaran motar, a daidai wannan lokaci ne Boko Haram suka bayyana.

Isarsu inda fasinjojin suke ke da wuya, sai yan ta’addan suka kwantar da guda uku daga cikinsu, suka musu yankan rago da adda, yayin da na hudunsu yake cikin mawuyacin hali a yanzu haka sakamakon raunin daya samu.

“Sun yi amfani da adda wajen daddatsa fasinjojin motar guda uku, yayin da na hudunsu yake fama da ransa a yanzu haka, mun same shi kwance cikin jini male-male, daga nan muka garzaya da shi zuwa wani asibiti dake cikin garin Maiduguri domin samun kulawa.” Inji shi.

Wannan hanya na Maiduguri zuwa Damturu ya yi fama da hare haren Boko Haram da dama a yan kwanakin nan, daga ciki har da harin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashin jami’in Soja dan asalin karamar hukumar Mai’aduwa ta jahar Katsina, Laftanar Nuruddeen Yusuf Mai’aduwa.

Kimanin kwanaki bakwai kenan da mutuwar wannan jarumin Soja a filin daga, wanda ya mutu a sanadiyyar harin kwantan bauna da mayakan Boko Haram suka kai ma tawagar Sojoji a kan wannan hanya.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

Sai dai ya gargadi yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel