Babbar magana: Allah ya nuna mini cewa ba za a rataye Maryam Sanda ba - Babban Fasto

Babbar magana: Allah ya nuna mini cewa ba za a rataye Maryam Sanda ba - Babban Fasto

- Wani malamin addinin Kirista kuma dan kasuwa mai suna Apostle Chris Omashola ya ce Maryam Sanda ba za ta mutu ta hanyar rataya ba

- A ranar Talatar da ta gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Maryam Sanda

- Malamin ya ce bai san dangin ta ba amma su ci gaba da addu'a don Ubangiji ya nuna mishi ba za ta mutu ta hanyar rataya ba

Wani malamin addinin Kirista kuma dan kasuwa mai suna Apostle Chris Omashola ya bayyana abinda ya hango game da Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta.

A ranar Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke zama a Maitama Abuja ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta sameta da laifin kisan kai.

Babbar magana: Allah ya nuna mini cewa ba za a rataye Maryam Sanda ba - Babban Fasto
Babbar magana: Allah ya nuna mini cewa ba za a rataye Maryam Sanda ba - Babban Fasto
Asali: Facebook

A yayin yanke hukunci a kan shari'ar, Mai shari'a Yusuf Halilu, ya kama ta da laifin abinda ake zargin ta da shi.

'Yan sanda sun zargi Sanda da sukar mijinta da fasasshiyar kwalba wajen karfe 3:50 na safiyar ranar 18 ga watan Nuwamba, 2017.

KU KARANTA: Na biya dala biliyan 1 ($1b) domin samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka - Mawaki Akon

Amma Apostle Omashola wanda cikin kwanakin nan ya bayyana 'wahayin' shi a kan mawaki Naira Marley, ya je shafin shi na tuwita a ranar Talata tare da sanarwa a kan Maryam Sanda ba za ta mutu ta hanyar rataya ba.

Kamar yadda ya ce, Ubangiji ya nuna mishi cewa Maryam Sanda ba za ta mutu ta hanyar rataya ba, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito

A shafin malamin, ya rubuta: "Ban san 'yan uwan Maryam Sanda ba. Jiya ne kawai na ci karo da maganar. Ta ci gaba da addu'a don na hango cewa za ta rayu. Ubangiji ba zai bar ta ta mutu ta hanyar rataya ba. Ban san ta yadda abin zai faru ba amma na hango hakan a wajen bauta. Ku taya ta da addu'a".

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng